Advert
Home Sashen Hausa Zuwaga Jaridun Katsina City News: Martanin wani Ma'aikacin Green House

Zuwaga Jaridun Katsina City News: Martanin wani Ma’aikacin Green House

Zuwa GA Jaridar Katsina City News

Martani Kan rubutun da kukai Kan Green House Enterprises Katsina.

Naga rubutunku na sharhin jaridun Katsina City News. Wannan yajawo hankalina Kan lallai nayi rubutu a matsayina na Dan jarida domin ghara ga wadanda sukai wannan rubutun, Don rubutun su na kasa shi Dalili ukku.

1. Ko dai Mai rubutun ya rasa sanin menene aikin jarida, wato (layman and unprofessional)

2. Ko yanada ra’ayi a rubutun na kashin kansa da yake son yacimmawa. Wato abinda a jarida ake cewa (Bias)

3. Ko matsoraci NE.

Bayanai na da nayi guda ukku zan tabbatar dasu da hujjojin da Yayi arubutunsa dake kasa.

korafe korafe da ya zayyana sune kamar haka:

“Daga cikin korafin, daya ya fito ne daga ‘yan kasuwa, wadanda suke nuna ana shirin aikata abin da bai kamata ba”

“Wani korafin kuma ya fito ne daga wasu dattawan Katsina da suka roki a fara rubutu da jawo hankali a kan lamarin, domin kuwa ana son rusa daya daga cikin gine-gine masu alaka da tarihin Katsina”

“Daya daga cikin ginin ya fi shekaru 100, domin shi ne dakin karatu na farko, dakin taro na farko da dakin kallo don jama’a na farko”

Da farko Ina son me rubutun yasani idan Muna da gidan gado Kuma akwai shuwagabanni a gidanmu masu hankali da Ilimi suka yanke shawara suka sayar dashi ga wani, Bisa ko wane Dalili, to a hankalce Mai sayene abin tuhuma ko Wanda yasayar.

“Na biyu, dakin karatun Jihar Katsina ya yi kadan, ya tsufa, yana bukatar karin fili don fadadawa, Jihar Katsina babbar Cibiyar Ilimin addinnin Musulunci da kuma Boko da wayewar siyasa, tana da ginin dakin karatu mafi kankanta a duk Nijeriya da yammacin Afrika”

Idan mukai duba da abinda ke Sama na marubucin yanuna cewa Gwammnatin Jihar Katsina Batasan Alkhairi da muhimmancin da shi yakawo a rubutunsa na Sama ba don Haka yadace ya Kai ta duk inda yadace a hukunta ta.

“Wata takardar da muke da ita, wasu na tattaunawa da Lauyoyi domin zuwa kotu a kan dakatar da shirin mallaka wa kamfanin Green House wannan gini”

Duba da abinda yafada a Sama mun Sanya ido muga menene zai aiwatar, za su Kai wadanda sukai laifin a hukunta su koko?

“Bayan mun yi nazarin takardun da muke da su, mun tattauna da masu korafin, mun ji ra’ayin jama’a da ‘yan kasuwa, mun kuma gabatar da namu binciken”

“A iya binciken da muka gudanar, mun gano Gwamnan Katsina, Alhaji Aminu Bello Masari bai da laifi a cikin wannan aikin da ake korafi akai”

“Mun fahimci cewa, Masari yana da wani irin kishi da saukin kai da zumudin ya aikata abin ci gaba da karfafa wa wanda ke neman kawo ci gaban Jihar Katsina gwiwa”

A wadannnan jawabannasa NE ya rusa duk tuhumar sa domin idan Har ka wanke Wanda da umarni su NE aka sayar da wannan wuri, to banga laifin Mai sayeba.

Tambayar da nake da ita anan:

– Tun da ka gano Mai girma Gwamna bashida laifi meyasa baka gamsar da Al’umma hujjojin da ka Gano cewa bashi da laifi, Don suma su amfana?

– kace kun fahimci Gwamna Masari nada wani irin kishi, to sayar da ita da Yayi Wannnan menene?

– yanzu abinda kake cewa ka wanke Gwamnati, Mai laifi shine hukumar gudanarwar Green House Enterprises Katsina Shagon?

Rubutunka ya nuna rashin kwarewa ko son ZUCIYA a aikace wato shine. (unprofessionality or bias ) idan kanason nuna kwarewa Sai ka fiddo duk bayanan da Gwamnati tayi da hanyoyin da tabi Har ta saida Wannnan waje sannan muhallin da kake son Green House Katsina tayi magana batayiba Sai ka fitar.

Sannan inda ka nuna son ZUCIYA, tun wuri ka Zare Gwannatin jihar Katsina kazama Dan ma’abanta.

KO Green House Enterprises Katsina, ba Al’umma jihar Katsina ke amfana da itaba ayi adalci a rubutun jarida.

Zan cigaba idan Ba’a gharaba.

Usman Ayuba masanawa

MSC media and mass communication.

Mun dauko ne daga rubutun da mai martanin yayi a shafin Facebook amma saboda adalci,muka buga shi a bisa shafin mu .

Masanawa yana cikin ma aikatan green house. Ra ayin sa ya kare ubangidansa ne

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

ADMISSION FORM IS AVAILABLE @ SILICON HEIGHT INTERNATIONAL COLLEGE KATSINA.

SILICON HEIGHT INTERNATIONAL, SCHOOL WISHES TO INFORM THE GENERAL PUBLIC THAT,THE SALE OF FORMS INTO NURSERY, PRIMARY AND SECONDARY IS STILL ONGOING. THE SCHOOL...

Gwamna Aminu Bello Masari ya buɗe taron shuwagabannin Majalisun jihohin Najeriya a Katsina…

Mai girma Gwamnan Jihar Katsina ya bude taron shugabannin majalisun Dokokin Jihohin Najeriya (36) a kwata na uku, da Jihar ta dauki bakunci. Taron da...

Jihar Katsina ta amshi bakuncin Kakakin majalisun Dokokin Jihohin kasar (36).

A cikin shirye, shiryen gudanar da Babban taron Kungiyar wanda ta sabayi lokaci bayan lokaci, domin tattauna al'amurran da suka shafi kasa. Taken taron na...
%d bloggers like this: