Gwamna Aminu Bello Masari yayi kira ga iyaye da kuma waɗanda Allah Ya ɗora ma alhakin rainon ‘ya’ya da su maida hankali ga kula da tarbiyyar su da kuma Ilimin su na addini da na zamani. Yin hakan zai ɗora rayuwar su kan turba ta gari kuma su tashi a mutanen kirki, nagari masu amfani ga al’umma.

Gwamnan yayi wannan kiran ne jiya a jawabin da ya gabatar wajen bukin Hawan Bariki na Sallah karama da ya gudana da hantsin yau a tsohon gidan gwamnati a nan cikin birnin Katsina.

Ya kara da cewa, mafi ƙarfin matsalar tsaron da muke fuskanta tana da tushe daga rashin tarbiyya da ilimi, domin kuwa kusan duk illahirin masu wannan munanan ayyuka sun rasa tarbiyya ne da kuma ilimi tun daga tasowar su har zuwa yau.

Alhaji Aminu Masari ya kuma bayyana tsananin damuwar shi kan yadda matasan dake zaune a karkara suke tsunduma cikin munanan ayyuka madadin su zama masu kwazon neman na kansu tare da zama masu amfani ga al’umma.

Gwamnan, ya kuma bayyana cewa gwamnatin tarayya a karkashin jagorancin Shugaba Muhammadu Buhari ta taka rawar gani sosai wajen kyautata rayuwar al’umma ta hanyoyi daban daban, musamman wajen bada tallafin kudi kai tsaye ga al’umma waɗanda suka fi tsananin bukata, ga kuma basussuka masu sauƙi da aka ba ƙananan ‘yan kasuwa. Sai kuma shirin N-Power da ya samar wa matasa sama da dubu goma sha huɗu ayyukan yi a wannan jiha.

Ya kara da cewa, yanzu haka, Gwamnatin Jiha, haɗin guiwa da ta Tarayya, tana gudanar da shirin ciyar da daliban Firamare sama da dubu ɗari bakwai (700,000) kyauta domin ƙarfafa masu guiwa wajen neman Ilimi.

A ƙarshe, Gwamnan yayi jinjina ta musamman ga al’ummar jihar Katsina bisa fahimta da kuma goyon bayan da suke ba gwamnati, tare da addu’ar Allah Yasa gwamnati mai zuwa tafi wannan taka rawa wajen kyautata rayuwar al’umma.

Tun farko a nashi jawabin, Maimartaba Sarkin Katsina Alhaji AbdulMumini Kabir Usman, ya bayyana munafunci da sonkai a matsayin na gidan gaba daga cikin matsalolin da suka addabi al’umma suka kuma hana mata samun ci gaban da ya dace.

Ya kara da cewa sai mun so juna don Allah kuma musa kishin addini da na kasa a zukatan mu sannan za mu sami nasara.

Alhaji AbdulMumini Kabir Usman ya kuma yi kira ga masu hannu da shuni da su rika fitar da zakka tare da bada ta yadda ya dace domin a sami saukin kuncin rayuwa da ake fama dashi.

Bukin na Hawan Bariki da ba a sami gudanar dashi ba tsawon shekaru biyu a jere da suka gabata saboda matsalar rashin tsaro da kuma ta Korona, yayi armashi sosai, kuma Mataimakin Gwamna Alhaji Mannir Yakubu, Shugaban Majalisar Dokoki ta jiha Alhaji Tasi’u Maigari Zango, Babban Jojin Jiha Maishari’a Musa Danladi Abubakar, Alkalin Alkalai na jiha Alhaji Dokta Muhammad Kabir Abubakar, Sakataren Gwamnatin Jiha Alhaji Muntari Lawal Katsina, ‘Yan Dokokin jiha,’ Yan Majalisar zartaswa ta jiha da kuma wasu manyan jami’an Gwamnati da kuma baki daga ciki da wajen jiha duk sun halarce shi.

A wani bangaren kuma, Gwamna Aminu Bello Masari yayi kira ga ‘yan siyasa da su dauki turbar da za ta tabbatar da ɗorewar siyasar da kuma zaman Najeriya ƙasa ɗaya al’umma ɗaya.

Gwamnan yayi wannan kiran ne jiya a fadar Gwamnatin Jiha, a jawabin da ya gabatar lokacin da ya tarbi bakuncin Gwamnan Jihar Ribas kuma mai neman zama ɗantakarar jam’iyyar PDP a zaben 2023 mai zuwa Mista Nyesom Wike.

Alhaji Aminu Bello Masari ya bayyana cewa fitowar mutane irin su Gwamna Wike neman takarar Shugaban ƙasa, alama ce dake nuna cewa ƙasar nan a ɗunke take ta yadda har kowa zai iya neman shugabancin ta ba tare da fargabar ɓangaren da ya fito ba.

Gwamna Masari, ya kuma yabawa Gwamna Wike a kan irin matakan da ya ɗauka wajen daƙile yunƙurin masu rajin kafa ƙasar Biyafara na hana su samun gindin zama a jihar ta Ribas, wanda da sun sami wannan dama to da Allah kadai Yasan halin da ake ciki yanzu a wannan yanki.

Haka kuma, ya bayyana cewa ba zai taɓa mantawa ba, da irin goyon bayan da ‘yan Majajiharlisar Tarayya masu wakiltar jihar Ribas suka bashi ba a lokacin da yake shugaban majalisar Wakilai ta Tarayya.

Yayi ma Gwamna Wike tare da tawagar tashi fatar alkhairi.

Tsohon Gwamnan Jihar Gombe Alhaji Ibrahim Hassan Dankwambo, wanda ke jagorantar rundunar yakin neman zaben Gwamna Wike, ya shaida ma Gwamna Masari cewa sun zo Katsina ne domin ganawa da wakilan jihar (delegates) da za su halarci taron jam’iyyar PDP na kasa domin neman goyon bayan su.

Shi kuwa Gwamna Wike yayi godiya ta musamman ga Gwamna Aminu Bello Masari domin irin tarbar da yayi masu duk kuwa da cewa basu sanar dashi kan lokaci ba. Ya kuma sha alwashin ba zai taba mantawa da wannan karamcin ba.

Duk dai a yau ɗin, Gwamna Aminu Bello Masari ya kai ziyarar ta’aziyya ga iyalan Marigayi Alhaji Tahir FadlAllah a gidan shi Nasarawa GRA a Kano.

Alhaji Tahir ya rasu ranar Juma’a da ta gabata a wani asibiti a kasar waje aka kuma yi jana’izar shi a ranar Asabar a fadar Maimartaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero.

Ya rasu yana da shekaru Saba’in da Hudu a duniya, ya bar mata da kuma zuriyya da dama. A cikin ‘ya’yan da ya bari akwai babban danshi Mohammed Tahir wanda ya tarbi Gwamna Masari tare da taimakon shuwagabannin al’ummar kasar Labanon dake Kano.

Alhaji Aminu Masari ya kuma yi addu’ar Allah Ya jikan shi da gafara kuma Yaba iyalai da sauran dangi hakurin jure wannan babban rashi, ya kuma ja hankalin su da su mika al’amurran su duka ga Allah domin lokaci gare ta kuma tana kan kowa.

Ya Allah Ka kawo mana dauki Ka yaye mana masifun da suka addabe mu Ka bamu damina mai albarka.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here