Zulum yaroƙi matasa da su shiga aikin banga domin magance matsalar tsaro tunda sojoji sun gaza

Gwamna Zulum na Barno yaroƙi matasa da suyiwa Allah su shiga Aikin sakai domin sukare rayuwar su da ta sauran Al'uma tunda Sojoji sungaza.

Zulum ya roki matasa su shiga aikin sa-kai a Borno

Gwamna Zulum

Gwamnan jihar Borno da ke yankin arewa maso gabashin Najeriya ya roƙi matasan jihar su shiga aikin sa-kai domin taimakawa a kawo ƙarshen ta’addanci a yankin.

Gwamna Zulum ya yi wannan kiran ne bayan kisan da wasu da ake tunanin ƴan Boko Haram ne suka yi wa manoma 43 a wani ƙauyen da ke kusa da garin Maiduguri fadar gwamnatin jihar.

Gwamnan kuma ya yi wannan kiran e lokacin da je ta’aziya da jaje ga mutanen garin Zabarmari da lamarin ya faru.

Sojojin Najeriya sun kasa kawo ƙarshen ayyukan Boko Haram a arewa maso gabas, inda aka kashe sama da mutum dubu goma.

A makon da ya gabata sojoji shida rahotanni suka ce an kashe a wani harin kwanton ɓauna a Borno.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here