Advert
Home Sashen Hausa Zulum Ya Bada Umarnin A Hukunta Wasu Ma'aikatan Lafiya Na Bogi

Zulum Ya Bada Umarnin A Hukunta Wasu Ma’aikatan Lafiya Na Bogi

Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum ya yi umarni a hukunta wasu ma’aikatan lafiya 21 da aka samu da gabatar da shaidar kammala karatu ta jabu da kuma ma’aikatan bogi 91.

Wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Isa Gusau, ya aike wa manema labarai ranar Litinin ta ambato gwamnan yana bayar da umarni a dauki matakin hukunci bayan wani kwamitin da aka nada domin tantance ma’aikatan ya gano mutum 21, ciki har da ma’aikatan jinya, suna gudanar da aiki ta hanyar amfani da sakamakon makaranta na jabu.

Kwamitin ya kuma gano ma’aikatan bogi 91 a ma’aikatu daban-daban a fadin jihar.

Shugaban kwamitin, Dr. Joseph Jatau ya bayyana cewa sun gano ma’aikatan bogi da masu amfani da takardun kammala karatu na jabu ne a rahoton da ya mika wa Gwamna Zulum ranar Litinin a Maiduguri.

Dr Jatau ya ce an gano fiye da N23m da ake kashewa bisa kuskure kowanne wata.

Ya kara da cewa sun gano yadda ake ci gaba da biyan wasu ma’aikata da suka mutu, ko wadanda suka yi ritaya da kuma wadanda ba sa zuwa aiki.

KATSINA CITY NEWShttps://www.katsinacitynews.com
Danjuma Katsina, Dan Jarida, Manazarci, Marubuci, Mamallakin Jaridun KATSINA CITY NEWS, JARIDAR TASKAR LABARAI, THE LINKS NEWS, a karkashin Kamfanin MATASA MEDIA LINKS NIGERIAN LTD

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

DRAFT APC CONVENTION TIMETABLE – Jan 16, 2022

1. January 17th - PMB Letter to CECPC on February National Convention and associated matters 2. January 18th -CECPC Meeting announcing National Convention date of...

Da ƊUMI-ƊUMI- Kotu ta umarci Rundunar Sojin Ƙasa da ta baiwa Nnamdi Kanu Naira biliyan 1

Wata Babbar Kotu da ke zaman ta a Umuahia ta baiwa Gwamnatin Taraiya da Rundunar Sojin Ƙasa da su baiwa Jagoran masu Rajin Samar...

THE RECONSTRUCTION OF THE APAPA – OWORONSHOKI – OJOTA EXPRESSWAY IS PROGRESSING EXPRESSLY!

https://www.facebook.com/101788642037662/posts/258361216380403/

Teenager kills man over football league supremacy

Teenager kills man over football league supremacy By Danjuma Michael, Katsina 19 January 2022   |   2:53 am A teenager, Idris Yusuf, 18, has allegedly killed a...