Zuckerberg ya tafka asarar dala biliyan 7 saboda katsewar Facebook

Facebook

Hanayen jarin Facebook ya faɗi da kashi 5.5 cikin 100, yayinda mai kamfanin, Mark Zuckerberg ya tafka asarar kusan dala biliyan 7 sakamakon katsewar shafin sada zumuntar a jiya Litinin.

Wannan katsewar ta shafi sauran shafuka mallakin Zuckerberg irinsu WhatsApp da Instagram.

Kamfanin mai karfin tattalin arziki a duniya ya rasa dimbin bilyoyin daloli tun bayan katsewarsa da misalin 4:42pm na yamma agogon Najeriya.

A cewar kididdigar NetBlocks, katsewar ta haifar da asarar dala miliyan 160 a kowacce sa’a guda.

Mutane sama da biliyan 2.9 ke amfani da shafin Facebook a faɗin duniya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here