Ziyarar Mataimakin Shugaban Kasa Farfesa Yemi Osibanjo ta Aiki a jihar Sokoto…

A yayin wannan ziyara ta wuni Daya Mataimakin Shugaban ƙasar Halartarci taron yaye Ɗaliban Jami’ar Jihar Sokoto Inda ya gudanar da ƙasida tare da yabawa Gwamnatin Jihar Sokoto akan aiyukanukan raya ƙasa da take yi.

Haka kuma a yayin wannan ziyara Osinbajo ya ziyarci wata cibiyar binciken Cutuka ta zamani watau (Diagnostic Center) Irin ta ta farko a Arewa maso yamma Mallakin Gwamnatin Jiha.

Kazalika Mataimakin Shugaban ƙasar ya ziyarci Asibitin koyarwa Mallakin Gwamnatin Jihar Sokoto wadda ake aikin ginin ta yanzu haka, dama Babbar Kotun Jihar wadda Gwamnatin tayima gyara na musamman tareda wadata ta da kayan aiki na zamani.

Ita dai wannan ziyara ta shafe tunanin cewa Gwamnatin Sokoto ta PDP ce shi Kuma Osinbajo dan APC ne.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here