Ziyarar da Sarkin Kano ya kai wa sarkin sarakunan Yarabawa

Sarkin Kano da Ooni na Ife

Mai martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya kai wa Ooni na Ife Ooni Adeyeye Enitan Ogunwusi Ojaja II ziyara a fadarsa ta Oodua da ke Ile-Ife.

Manyan Sarakunan biyu na Najeriya sun ƙarfafa dangantaka da amintakar da ke tsakaninsu wacce suka ce ta samu asali tun daga iyayensu.

Sarkin Kano da Ooni na IfeCopyright: Ooni’s Palace

Ooni Ogunwusi wanda ɗaya daga cikin shugabannin majalisar sakunan gargajiya ta Najeriya ya ce ya yi farin cikin ziyarar da sabon Sarki ya kawo masa

“Na yi farin ciki da cewa sabon Sarkin Kano wanda ba baƙo ba ne a wannan fada ya yarda cewa mu rike al’adun mahaifanmu; wanda na gada Ooni Okunade Sijuwade da marigayi Sarki Ado Bayero da marigayi Obi na Onitsha aminan juna ne kuma abotarsu na daga cikin moriyar da muke ci a Najeriya,” in ji Oni na Ife.

A nasa jawabin, Sarkin Kano ya yaba wa Ooni Ogunwusi na yin jagoranci a ƙasar ƙabilar Yarabawa. Ya kuma ce dangantakarsu za ta ƙara zumunci da haɗin kai da ci gaba tsakanin ƙabilar yarabawa da kuma takwarorinsu na arewacin Najeriya.

Sarkin Kano da Ooni na Ife

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here