Alhaji Ɗahiru Mangal Ya Ziyarci Shugaban Jam’iyyar APC Na Ƙasa Sanata Abdullahi Adamu A Gidan Shi Dake Abuja

Daga Comr Nura Siniya

Hamshaƙin Ɗan kasuwa shugaban kamfanin sufurin jiragen sama na Max-Air ƙashin bayan siyasar jihar katsina Alhaji Ɗahiru Bara’u Mangal, ya ziyarci Shugaban Jam’iyyar APC na ƙasa Sanata Abdullahi Adamu, a gidan shi da ke birnin tarayya Abuja.

Alhaji Ɗahiru Mangal, ya ziyarci Sanata Abdullahi Adamu, ne domin taya shi murna bisa ga nasarar da ya samu na zama sabon shugaban jam’iyyar APC na ƙasa.

A ƙarshe Sanata Abdullahi Adamu, ya godewa ziyarar da Alhaji Ɗahiru Mangal ya kai mashi domin ƙara ƙarfafa zumuncin da ke tsakaninsu tare da bayyana shi a matsayin babban Jigo na Jam’iyyar a Najeriya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here