Gwamnan jihar Barno Babagana Umara Zulum ya tsantsame hannun sa daga alaka da DCP Abba Kyari ya ce shi kam bai ma san wani wanda ake kira Kyari ba ballai ya ziyarci gidan sa.

Gwamna Zulum na wannan maganar ne bayan da ake yawo da wani faifan bidiyo mai nunar da gwamna Zulum ya kai wa DCP Abba Kyari ziyara a gidan sa bayan da yake cikin matsin bincike kan zargin da kasar Amurka ke masa na karbar cin hanci daga hannun fitaccen dan damfarar nan Hushpuppi.

Gwamna Zulum ta bakin mai magana da yawun sa Dakta Isah Gusau ya bayyana cewar, shi kam sam baida alaka da DCP Abba Kyari ya kuma nemi Abba Kyari cikin hanzari ya fito ya karyata bidiyon.

Dakta Isah Gusau ya ce bidiyon da ake yawo dashi an dauke shi ne tun ranar 30-06-2021 lokacin da shi DCP Abba Kyari ya kai wa Kashim Shattima ziyara duba lafiyar sa bayan da ya dawo daga kasar Ingila wajen jinya saboda haka ya ce bidiyon bana yanzu bane kuma gwamna Zulum ko kadan baida alaka da Kyari.

DCP Abba Kyari na cigaba da fuskantar barazana tun bayan da Hushpuppi ya ce ya bashi cin hanci kuma ya karba wanda kasar Amurka ke neman DCP Abba Kyari don binciken sa wanda kuma hakan ne yasa kowa yake yanke alaka da DCP Abba Kyari sabida gujewa zargi.

Gwamnan jihar na Barno Babagana Umar Zulum ya musanta bidiyo ya kuma ce shi kam kwata-kwata baida alaka da DCP Abba Kyari.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here