Home Sashen Hausa Zanga-zangar EndSars ta rikiɗe zuwa rikici a Abuja

Zanga-zangar EndSars ta rikiɗe zuwa rikici a Abuja

Zanga-zangar EndSars ta rikiɗe zuwa rikici a Abuja

Endsars
Image caption: Mutane na cikin fargaba a birnin tarayyar

Ana fargabar an samu asarar rayuka yayin zangar-zangar da ta koma tarzoma a lokacin da wasu da ake zargin ‘yan banga ne suka kai hari kan masu jerin gwano a wasu sassan Abuja.

An kuma yi ƙone-ƙonen dukiya da lalata ababen hawa yayin zanga-zangar.

Abokin aikinmu Zahraddeen Lawan ya ziyarci daya daga cikin wuraren da lamarin ya afku wato rukunin shgunan Banex da ke Wuse a Abuja, kuma ya tabbatar da cewa ya ga kusan mutum huɗu a kwance magashiyyan a ƙasa.

Sannan wasu rahoranni sun tabbatar da cewa a Unguwar Apo Mechanic ma an smu hargitsi tsakanin Hausawa masu sayar da kayan miya da ƴan ƙabilar Ibo masu gyaran motoci.

Wata mazauniyar unguwar da ta dawo daga bulaguro da nufin isa gidanta, ta shaida wa BBC cewa dole ta sa ta juya ta koma cikin gari.

”Mun hango hayaƙi na tashi sannan an yi wa masu sayar da kayan miya da kayan marmari ɓarna sosai su kuma masu gyaran mota su ma an yi musu ɓarna an ƙona shagunansu.

”Na hango hayaƙi yana ci sakamakon ƙone-ƙone da aka yi. Dole ta sa muka juya don gudun kar abin ya rutsa da mu.”

Har yanzu dai hukumomi ba su ce komai ba dangane da lamarin.

Sai dai mazauna birnin na cike da fargaba sosai na tsoron abin da ka je ya zo.

Endsars

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

Hukumar Tsaron farin kaya ta DSS ta gayyaci shugaban masu safarar kayan abinci zuwa kudu

Yanzu yanzu: Hukumar tsaron farin kaya ta DSS ta gayyaci Shugaban masu safarar kayan Abinci bisa dalilin rufe hanya da hana kai kayan Abinci...

Zan Kashe Duk Wani Dan Siyasa Da Ya Fito Don Takara 2023- Sunday Igboho Sunday Adeyemo wanda aka fi sani

Zan Kashe Duk Wani Dan Siyasa Da Ya Fito Don Takara 2023- Sunday Igboho Sunday Adeyemo wanda aka fi sani da Igboho ya yi gargadin...

Yajin aikin ‘yan kasuwa ya tashi farashin kayan abinci a kudancin Najeriya

Yajin aikin 'yan kasuwa ya tashi farashin kayan abinci a kudancin Najeriya Yajin aikin da dillalan kayan abinci suka fara na ƙungiyar Amalgamated Union of...
%d bloggers like this: