Ministan Shari’a kuma Babban Lauyan Gwamnati, Abubakar Malami, ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar Gwamnan Jihar Kebbi a zaben 2023 mai zuwa.

Malami ya bayyana hakan ne a gaban magoya bayansa a Birnin Kebbi ranar Litinin, inda ya ce ba zai ba su kunya ba.

Ya ce, “Idan Allah a cikin rahamarSa Ya amince, kuma komai ya tafi daidai, zan tsaya takarar Gwamnan Jihar Kebbi, a matsayina na dan siyasa. Ina neman taimakon ku.

“Ina sanar da ku cewa zan tsaya takara, saboda haka ina neman addu’o’inku. Ba ni da tarihin cin amana kuma ba zan ci amanarku ba, hidimta muku,” kamar yadda ya shaida wa magoya bayan nashi.

Ministan ya dai yi alkawarin yin aiki ba dare ba rana don farfado da kimar Jihar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here