Zan Sadaukar Da Kujerata Domin Zaman Lafiyar Katsina, Cewar Sarkin Katsina

Mai Martaba Sarkin Katsina Alhaji Abdulmuminu Kabir Usman, ya bayyana cewar zai iya sadaukar da kujerar shi, idan har hakan zai sanya a samu zaman lafiya a Jahar Katsina.

Alhaji Abdulmuminu Kabir Usman ya bayyana haka a lokacin da yake jawabi, a taron tsaro da ya shirya domin gano hanyoyin da za’a samar da dauwammen zaman lafiya a jahar Katsina.

Taron wanda ya gudana a ɗakin taro na Hukumar kula da ma’aikatan Ƙananan Hukumomi ta Jahar Katsina, ya samu halartar Hakimai, Alƙalai, da Lauyoyi, da Limamai, da Jami’an tsaro da Ƴan Bijilante, da Maiba Gwamna Shawara na Musamman akan harkokin tsaro Alhaji Ibrahim Katsina da sauran su.

Mai Martaba Sarkin Katsina Alhaji Abdulmuminu Kabir Usman
ya ce an shirya taron ne domin tattaunawa akan matsalolin tsaro dake cigaba da ƙaruwa a jahar, tare da gano hanyoyin da za’a magance su a Jahar Katsina.

Uban Ƙasar ya bayyana damuwa na yanda wasu Alƙalai, da Lauyoyi, da ƴan ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adam suke kare ƴan ta’adda a Kotu, sai ya buƙace su da suji tsoron Allah a dukkanin abinda suke yi na rayuwa.

Mai Martaba Sarkin ya umarci Hakimai da su kafa wani asusu
daza’a bada tallafi domin amfani dasu, wajen inganta tsaro a yankunan su, inda yace masarautar tuni ta fara haka, kuma an samu kuɗaɗe masu yawa da a halin yanzu za’ayi amfani dasu wajen tsaro.

Alhaji Abdulmuminu Kabir Usman ya nanata buƙatar dake akwai na ɗaukar matakin gaggawa ga ƴan bindiga daɗi, da masu fyaɗe da sauran ƴan ta’adda, wanda acewar sa hakan zai samar da tsaro a jaha dama ƙasa baki ɗaya.

Maiba Gwamna Shawara na Musamman akan harkokin tsaro Alhaji Ibrahim Katsina yayi jawabi akan ɗumbin nasarorin da aka cimmawa, biyo bayan dokar tabbatar da tsaro da gwamnatin Jahar ta sanya.

Alhaji Ibrahim Katsina yace Gwamnatin Jahar ta ɗauki ƴan ƙungiyar Bijilante guda 3000 domin marawa jami’an tsaro baya wajen samar da tsaro a jahar.

Kwamishinan Ƴan sanda na Jahar CP Sanusi Buba wanda ya samu wakilcin Mai magana da yawun Rundunar Ƴan Sandan Jahar SP Gambo Isah, ya ɓuƙaci Al’umma dasu cigaba da baiwa jami’an tsaro goyon baya da haɗin kai domin samar da tsaro a jihar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here