Zamufara zanga-zanga a dukkan Arewacin Najeriya gobe alhamis-CGN

Zamufara zanga-zanga a dukkanin fadin arewacin Najeriya a gobe alhamis-CGN

DA DUMI-DUMI | Zamu fara zanga-zanga a fadin jihohin Arewacin Najeriya gobe Alhamis – CGN.

Gamayyar kungiyoyin Arewa (CGN) wanda Alhaji Ashir Nastura ke jagoranta, tace zata fara gudanar da zanga-zanga a fadin Arewacin Najeriya domin kira da babbar murya ga gwamnatin Muhammadu Buhari da ta kawo karshen kashe-kashen rayukan al’umma, garkuwa da mutane, hare-haren ta’addanci da kuma Boko Haram a yankin Arewa kamar yadda ta kawo karshen SARS.

Zanga-zangar mai taken #EndInsecurityNow zata fara gudana ne a gobe Alhamis 15 ga watan Oktoba 2020 a dukkan jihohin Najeriya.

A don haka wannan kungiya ke kira ga duk wani dan Arewa mai kishin kawo karshen ta’addanci da kashe-kashen rayukan al’umma a dukkan jihohin Arewa ya fara rubuce-rubuce a kafafen sada zumuntar zamani yana kiraye-kiraye ga gwamnati ta kawo karshen matsalar tsaro a yankin Arewa da Hashtag #EndInsecurityNow.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here