Gwamna Aminu Bello Masari ya bada tabbacin cewa duk wanda ya rasa shagon shi sakamakon ibtila’in gobarar da akayi a babbar kasuwar Fatima Baika dake a nan cikin birnin Katsina zai sami sabon shago da zarar an kammala gyaran kasuwar.

Gwamnan ya bada wannan tabbacin ne a cikin jawabin shi na kaddamar da kwamitin da zai raba tallafi ga ‘yan kasuwar da suka tafka asara sanadin waccan gobara.

Ya bayyana cewa ba za a sake yarda bata tsarin kasuwar ba ko kuma yin gini ba tare da cika ka’idojin aiki ba. Haka kuma duk wani da yake da bukatar ya shiga ko kuma yayi aikin da kan shi to ana maraba da hakan amma dole yabi tsarin tsawirar da aka fitar.

Gwamnan ya kara da cewa za ayi kokarin ganin duk wanda yayi asara ya sami kashi arba’in bisa dari (40%) na dukiyar da ya rasa.

Alhaji Aminu Bello Masari ya kuma bayyana cewa an dauko wakilci daga kowane bangare na kungiyoyin al’umma da ma’aikata domin tabbatar da anyi adalci wajen wannan aiki.

Wadanda kuma suke da bukatar bada shawara to Kofar wannan kwamiti a bude take domin hakan.

Wannan kwamitin dai yana karkashin jagorancin Barista Ahmed Usman El Marzuk Kwamishinan Shari’a na jiha,

yakuma kunshi wasu ‘yan Majalisar zartaswa ta jiha da kuma kungiyoyin sa kai, na kwadago da kuma na’ yan kasuwa.

A wani bangaren, Gwamna Aminu Masari yayi kira ma’aikatan Gwamnatin Jiha da su rike amanar aikin su tare da bada gudummawa wajen kawo ma wannan ci gaban da take bukata. Yayi wannan kiran bayan da ya rantsar da sabbin manyan sakatarori guda biyu.

Ya kuma yi masu fatar alkhairi tare da addu’ar Allah Yai masu jagoranci.

Wadanda aka rantsar din su ne Alhaji Abdullahi Abubakar (Abdullahi Gagare) da kuma Barista Hassan Yusuf.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here