Zamu Shiryawa Babban Hafsan Sojojin Najeriya, Attahiru Liyafa A Kaduna – El-Rufai

Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya mika sakon taya murna ga sabon Babban Hafsan Sojojin Najeriya, Manjo-Janar Ibrahim Attahiru.

El-Rufai ya bayyana cewa zabin Attahiru zabi na gari yana mai cewa ya zo a daidai kasa na fama da karauniya da faɗi tashin kawo karshen hare-haren ƴan bindiga da kuma sace-sacen masu garkuwa da mutane.

Bayan haka gwamnan ya kuranta Attahiru a matsayi zakakumin dakaren Soja wanda zai kawo sauyi mai ma’ana a ayyukan samar da zaman lafiya da gwamnati ta saka a gaba.

Sannan kuma gwamnan ya kara da cewa gwamnati da mutanen kasar haf Kaduna za su shirya wa Babban Hafsan Sojojin Najeriyan ƙasaitaccen buki domin nuna farincikin gwamnati da mutanen Kaduna na nada shi da shugaba Muhammadu Buhari yayi.

A karshe ya jinjinawa wa shugaban Kasa, Buhari bisa kyawawan nazari da yayi wajen zakulo zaratan sojin da ya nada manyan Hafsoshin Tsaron kasar nan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here