Wasu fusatattun matan Neja-Delta a karkashin kungiyar Fafutukar Matan Neja-Delta (WWND) sun baiwa shugaban kasa Muhammadu Buhari wa’adin mako guda daya kaddamar da kwamitin gudanarwa na hukumar raya yankin Neja-Delta, ko kuma su fito zanga-zanga su mamaye titunan yankin a tsirara ba kaya a jikin su ba tare da wata matsala ba.

Mambobin kungiyar WWND da suka hada da masu fafutuka, masu ra’ayi da kwararru a fadin jihohi tara na yankin, a wata sanarwa a ranar Litinin bayan wani taro da suka yi a garin Fatakwal na jihar Ribas, sun koka da cewa, “an dauki mutanen yankin ba komai ba kuma abin banzatarwa da dadewa, an yi watsi da su a matakai daban-daban.”

Matan yankin Neja-Deltan, tare da rakiyar ‘yan kungiyar Integrity Friends for Truth and Peace Initiative (IFTPI) da suka halarci taron domin ba su goyon baya, sun ce rashin samar da wata kwakkwarar hukumar NDDC ya kara jefa yankin cikin talauci saboda su ke cikin wahala.

Shugabar hukumar ta WWND, Oney Nwadighi, wadda ta karanta sanarwar a karshen taron, ta ce hakurin matan ya kare, don haka suka kuduri aniyar yin wani abu a kan halin da suke ciki.

Wani bangare na sanarwar yace; “Abin takaici, mazan mu da ubanninmu sun yi kasa a gwiwa sun yi barci yayin da yankinmu ke cikin duhun rashin ci gaba a daidai wannan lokaci.

“A kan haka, mun rike da Sanata Godswill Akpabio, mai kula da harkokin Neja Delta, da cikakken alhakin tabarbarewar al’amuran yankin.

“Muna bukatar Gwamnatin Tarayya, a cikin kwanaki bakwai masu zuwa, ta samar da kwamitin gudanarwa na NDDC ciki har da majalisar ba da shawara ga gwamnonin hukumar daidai da tanadin Dokar NDDC, idan a ka kasa yin haka, bamu da wani zabi face mu fito zanga-zanga mu mamaye titunan yankin Neja-Delta tsirara don mu nuna fushi da bacin ran mu.

“Ya isa haka. Ba za mu ƙara ɗaukar wannan ba. Gwamnatin Tarayya da Sanata Godswill Akpabio ba za su iya sake daukar yankin Neja-Delta ba.

“Zamu fito tsirara mu dage a kan hakkinmu a matsayinmu na masu daukar nauyin yankin mu, in yaso su shirya su kashe mu duka,” sanarwar ta kara da cewa.

Jaridar Sokoto

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here