Zamfara: Iyayen Daliban Da Aka Sace A Makarantar Jangebe Sun Bi Sawun Yaransu Cikin Daji

Iyaye da kuma ‘yan uwan ɗaliban da aka sace a makarantar sakandare ta GGSS Jangebe a Jihar Zamfara sun bi sawun ‘yan bindigar cikin daji.

Wasu daga cikin iyayen sun shaida wa BBC Hausa cewa sun yanke shawarar bin sawun yaran nasu ne da zummar ceto su daga hannun miyagun.

“Gaba ɗaya garin Jangebe ne muka tasan ma ɓarayin, ko mu dawo da ranmu ko a kashe mu,” a cewar wani da aka sace ƙannensa biyu.

“An ce mana an gan su (‘yan bindiga) suna tafiya da yaran a cikin daji, saboda haka mutunen garin Jangebe kusan 3,000 sun fito sun ce za su bi sahunsu.”

Ƴan bindiga sun sace ɗalibai mata kusan 300 a jihar Zamfara
A daren Alhamis ne ‘yan bindigar suka yi wa makarantar tsinke, wadda ta kwana ce.

Mahaifin daya daga cikin daliban da kuma wani malami da ke makarantar lokacin da aka sace daliban sun tabbatar wa BBC aukuwar lamarin.

Kazalika wani ganau ya ce an tabbatar da sace mata fiye da 300 ne sakamakon kirga dukkan ‘yan makarantar da suka rage bayan barayin sun sace daliban.

Har yanzu rundunar ‘yan sandan jihar da ma gwamnatin Zamfara ba su ce komai a kan batun ba.

Garin Jangebe wanda ke cikin Ƙaramar Hukumar Talata Mafara, na da nisan kilomita 89 daga Gusau babban birni jihar ta Zamfara.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here