Rikicin siyasa a Jihar Zamfara ya ƙara ruruwa bayan da Mataimakin Gwamnan jihar, Mahdi Aliyu ya ke gayawa Gwamna Bello Matawalle cewa an ja layin yaƙi tsakanin su.

Da ya ke jawabi a ƙarshen zaɓen shugabannin jam’iyar PDP na jiha a jiya Litinin da daddare, Mataimakin Gwamnan ya ce “yanzu fa ba ɗaga ƙafa.”

“Da ga yau, an ja layin yaƙi. Idan an kashe mutane kuma gwamnati ta yi shiru, to mu za mu yi magana. Idan gwamnati ta ƙi bude makarantu, za mu yi magana.

“Hakazalika za mu magantu idan manoma su ka kasa zuwa gonakin su ko idan a ka ƙi ginawa al’umma tituna. Za mu ci gaba da sukar gwamnati a kan ba daidai ba da ga yanzu har zuwa lokacin da za mu karɓi mulki,” in ji Aliyu.

Haka-zalika, Mataimakin Gwamnan ya nuna damuwa a kan “irin gallazawa PDP” da a ke yi a jihar tun bayan da gwamnan ya sauya sheƙa zuwa APC.

Aliyu ya suffanta PDP a matsayin jam’iya mai bin doka, inda ya nuna cewa kundin tsarin mulki ya baiwa jam’iyar damar samuwa a Zamfara.

Ya yi alƙawarin gina sabuwar PDP mai cike da zaƙaƙuran matasa ma su ilimi.

Ya ƙara da cewa hakan shi zai sanya jam’iyar ta kwaci mulki a Zamfara a 2023.

Aliyu ya kuma yi kira ga gwamna Matawalle da ya sakarwa PDP mara ya maida hankali a kan magance matsalolin da ke damun jihar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here