Advert
Home Sashen Hausa ZAMAN KOTUN BILKI ƘAIƘAI DA GWAMNATIN AMINU BELLO MASARI, Alhamis 19/11/2020

ZAMAN KOTUN BILKI ƘAIƘAI DA GWAMNATIN AMINU BELLO MASARI, Alhamis 19/11/2020

ZAMAN KOTUN BILKI ƘAIƘAI DA GWAMNATIN AMINU BELLO MASARI, Alhamis 19/11/2020

Nura Press @katsina city news

Ajiya Alhamis ne,19/11/2020 babbar kotun jihar katsina ta zauna Shari’ar Hajiya Bilkisu Mohammed Ƙaiƙai da Gwamnatin jihar a ƙarƙashin Offishin kwamishinan Shari’a na jihar katsina, Antoni janaral El-marzuq, Inda ake tuhumar tsohuwar mai bawa Gwamna Ibrahim Shema shawara kan Ilimin ƴaƴa mata Hajiya Bilikisu Muhammad ƙaiƙai, da al’mundahana da wasu kuɗaɗe a ƙarƙashin ofishinta.

Bayan zama na farko ya gudana a 12/11/2020, inda Alƙalin kotun mai lamba 4, mai shara’a Bawale ya ɗage zaman saurararen karar zuwa 19/11/2020.

Lauyoyin gwamnatin da na Hajiya ƙaiƙai sun fafata, inda Alkalin ya sake ɗage zaman saurararen Shari’ar zuwa 2 ga watan Disambar wan’nan shekarar.

Bayan kammala zaman kotun, Ƙaiƙai takuma amsa wani Kira daga ofishin binciken laifuffuka, inda nan ma ake neman bayanin wasu kudaden.

Abinda wasu masu nazari ke tambaya shine, shin dama ana tuhuma 2 ga  ma’aikacin Gwamnati alokaci guda, akaishi kotu kuma akaishi ofishin ‘yan sanda?  Hajiya Bilkisu Muhammad ƙaiƙai dai ta taɓa amsa kiran Binciken Hukumar EFCC bayan da wadin mulkin su na Gwamnatin PDP ya ƙare, ana zargin bita da ƙullun da ake mata baya rasa nasaba da wata hira da gidan Rediyon DW hausa inda take cewa yakamata Gwamnatin jihar katsina ta dubi halin da mata ƴan gudun hijira suke ciki na yawon barace barace bayan kashe mazajen su, acewar ta bai kamata Gwamnatin katsina ta gina gidaje da shaguna ga ƴan ta’addan da suka kashe mazajen su ba.

Agefe guda wasu suna zargin Ƙaiƙai da bawa mai kwarmato Mahadi Shehu wasu bayanan sirri duk da cewa bata riƙe da wani muƙami a Gwamnatin mai ci, ta Aminu Bello Masari.

Hajiya Bilikisu ƙaiƙai dai ta hannun daman tsohon sanata mai neman takarar Shugabancin ƙasa Alhaji Ahamad Sani Yariman Bakura, itace jigo a wan’nan ƙungiyar ta YSO ta Bakura a jihar katsina, abin da wasu ƴan jam’iyyar adawa ke tambaya shine: miyasa Gwamnati bazata nemi Hajiya ƙaiƙai ba a jam’iyyance su tattauna kasantuwar ta ƴar jam’iyyar APC mai mulki.

KATSINA CITY NEWShttps://www.katsinacitynews.com
Danjuma Katsina, Dan Jarida, Manazarci, Marubuci, Mamallakin Jaridun KATSINA CITY NEWS, JARIDAR TASKAR LABARAI, THE LINKS NEWS, a karkashin Kamfanin MATASA MEDIA LINKS NIGERIAN LTD

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

WHAT SECTORS OF THE GLOBAL ECONOMY DID NIGERIA ENGAGE MORE IN LAST YEAR?

WHAT SECTORS OF THE GLOBAL ECONOMY DID NIGERIA ENGAGE MORE IN LAST YEAR? #PositiveFactsNG This infograph below shows us what sectors of the global economy Nigerian...

NEW INFRASTRUCTURE FOR THE NIGERIAN NAVAL BASE IN AKWA IBOM STATE!

https://www.facebook.com/101788642037662/posts/257872623095929/