Zaman Fargaba A Harabar Majalisar Dokoki Ta Kasa An tsaurara matakan tsaro a muhimman wurare

Boko Haram suna dab da shiga birnin tarayya Abuja, inji gwamnan Neja

Akwai fargaba a safiyar yau Alhamis yayin da jami’an tsaron dake aiki a majalisar dokoki ta kasa suka tsaurara matakan tsaro a mashigar majalisar, ‘yan majalisa da mataimakansu da maziyarta majalisar suna shan tsauraran cikakken bincike a kofofin shiga harabar majalisar kafun samun damar shiga.

Ba sani ba sabo, dukkan ma’aikatan majalisar da ‘yan jaridar da ke aiki a harabar ta sai sun nuna katin shaidar aiki kafin a ba su damar shigewa, kamar yadda shafin Madubi-H ya nakalto.

Tsaurara tsaron ba zai rasa nasaba da barazanar tsaro a kasar ba, da kuma ikirarin da Gwamnan Neja ya yi na cewa mayakan Boko Haram suna dab da babban birnin tarayya Abuja.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here