Advert
Home Sashen Hausa Zagayen Juyayin 'Yan Shi'a: Jami'an tsaron Najeriya sun buɗe wuta a Abuja

Zagayen Juyayin ‘Yan Shi’a: Jami’an tsaron Najeriya sun buɗe wuta a Abuja

Zagayen Juyayin ‘Yan Shi’a: Jami’an tsaron Najeriya sun buɗe wuta a Abuja…

Rahotanni dake shigomana daga Abuja nacewa, gamayyar Jami’an tsaro, na Najeriya sun buɗe wuta ga ‘yan shi’a masu Tattaki don nuna juyayin kashe Sayyiduna Husain,

Bayan harba Hayaƙi me sa hawaye daga bisani jami’an tsaron suka cigaba da antaya Harsashi mai rai, inda ake kyautata zaton rasa rai ɗaya da Jikkata da dama daga cikin ‘yan shi’an.

Kamar ko wace shekara, ‘yan shi’a Al’majiran Sheikh Ibrahim El’zakzaky dake fadin Najeriya suna gudanar da Tattakin a wasu yankuna zuwa Zariya, inda suka takaita shiga Zariyar tun bayan kisan da sojoji sukayi masu, inda suka kama Malamin nasu Sheikh Zakzaky, kodayake wata Babbar Kotu a kaduna ta wankeshi bayan kwashe tsawon shekaru shida a tsare.

Abinda Al’uma da dama ke tambaya shine, shin ko mi yasa akewa ‘yan shi’an kisan gilla duk da halin da ƙasar take ciki na Ta’addanci da garkuwa da mutane domin neman kuɗin fansa?

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

ADMISSION FORM IS AVAILABLE @ SILICON HEIGHT INTERNATIONAL COLLEGE KATSINA.

SILICON HEIGHT INTERNATIONAL, SCHOOL WISHES TO INFORM THE GENERAL PUBLIC THAT,THE SALE OF FORMS INTO NURSERY, PRIMARY AND SECONDARY IS STILL ONGOING. THE SCHOOL...

Gwamna Aminu Bello Masari ya buɗe taron shuwagabannin Majalisun jihohin Najeriya a Katsina…

Mai girma Gwamnan Jihar Katsina ya bude taron shugabannin majalisun Dokokin Jihohin Najeriya (36) a kwata na uku, da Jihar ta dauki bakunci. Taron da...

Jihar Katsina ta amshi bakuncin Kakakin majalisun Dokokin Jihohin kasar (36).

A cikin shirye, shiryen gudanar da Babban taron Kungiyar wanda ta sabayi lokaci bayan lokaci, domin tattauna al'amurran da suka shafi kasa. Taken taron na...
%d bloggers like this: