Advert
Home Sashen Hausa Zaben Shuwagabannin Jam'iyyar APC a Katsina... Tsohon Ciyaman yasa mu kware Fostar...

Zaben Shuwagabannin Jam’iyyar APC a Katsina… Tsohon Ciyaman yasa mu kware Fostar Dan’takara:

Zaben Shuwagabannin Jam’iyyar APC a Katsina… Tsohon Ciyaman yasa mu kware Fostar Dan’takara:

Zaharaddeen Ishaq Abubakar @Katsina City News

An Ja Zare tsakanin masu neman kujerar Shugabancin Jam’iyyar APC a Katsina,

Malam Bala Musawa da tsohon Ciyaman Malam Shitu S. Shitu sune suka bayyana aniyarsu ta son Kujerar Jam iyyar APC matakin jiha, Inda wasu daga cikin Mutanen Jihar ta Katsina suka bayyana ra’ayinsu akan Malam Bala Musawa ya maye gurbin Malam Shitu da ya kwashe shekaru kusan Shida a matsayin Shugaban Jam’iyyar.

Sai dai abin baima wasu masoya tsohon Ciyaman Shitu dadi ba, inda suka so atafi babu adawa, ma’ana Angulu ta koma gidanta na tsamiya duba da, dukkanin su, daga Jam’iyya daya suka fito, Uwa ɗaya uba ɗaya.

Amma a ɓangaren Bala Musawa Kuwa, cewa suke, ai ba haka ake Dimokuraɗiyyar ba, kuma su bazasu yarda da karfa-karfa ba, saboda shekara shida, idan ma Alheri ne, sungani kuma suna bukatar Canji a cikin Canji.

Wannan tankiya da tata ɓurza bata yiwa ‘yan gani kashenin Mutanen biyu daɗi ba, a dalilin haka ma yasa, Tsohon Ciyaman ya aiko a cire duk wata Fosta ta abokin hamayyarsa daga Ofishin jam’iyya, kamar yanda wani matashi kuma daya daga cikin masu kula da Ofishin jam’iyyar ya shedama Katsina City News “An aiko ance tsohon Ciyaman yace mai girma Gwamna yace acire Fostar Bala Musawa, tunda baici zaɓe ba, Mu kuma mukace to Fostar kowa ma acireta daga Ofishin tunda ba’ayi zaɓe ba”

Usman Musa Liba kamar yanda ya bayyanamana sunansa, yamana korafi akan halin da suke ciki, na ko inkula inda yace ance su kware fosta za’a sallamesu amma ko Sisin kwabo Malam Shitu bai aiko masu dashi, ba. Liba ya kara kira da cewa Don Allah Tsohon ciyaman ya taimaka ya dunga zuwa Ofis (dukda ya sauka) idan har bai ɗauko wani abu ya basu ba, to na tare dashi zasu basu, inda yace, Aiken mai girma Gwamna ma bai taba zuwa wajensu ba Balle na Malam Shitu tsohon Ciyaman.

Yace sunyi karatu, an amshi Takardunsu amma kullum sai romon baki, da canza magana, abinci ma su ke saima kansu.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

ADMISSION FORM IS AVAILABLE @ SILICON HEIGHT INTERNATIONAL COLLEGE KATSINA.

SILICON HEIGHT INTERNATIONAL, SCHOOL WISHES TO INFORM THE GENERAL PUBLIC THAT,THE SALE OF FORMS INTO NURSERY, PRIMARY AND SECONDARY IS STILL ONGOING. THE SCHOOL...

Gwamna Aminu Bello Masari ya buɗe taron shuwagabannin Majalisun jihohin Najeriya a Katsina…

Mai girma Gwamnan Jihar Katsina ya bude taron shugabannin majalisun Dokokin Jihohin Najeriya (36) a kwata na uku, da Jihar ta dauki bakunci. Taron da...

Jihar Katsina ta amshi bakuncin Kakakin majalisun Dokokin Jihohin kasar (36).

A cikin shirye, shiryen gudanar da Babban taron Kungiyar wanda ta sabayi lokaci bayan lokaci, domin tattauna al'amurran da suka shafi kasa. Taken taron na...
%d bloggers like this: