Advert
Home Sashen Hausa ZABEN SHUGABANNIN APC NA KATSINA.....AN SAMU YAN TAWAYE

ZABEN SHUGABANNIN APC NA KATSINA…..AN SAMU YAN TAWAYE

 


….Wani na neman chairman
…wani organizing secretary

Muazu hassan @Katsina City News

Ana sauran awowi a fara taron tabbatar da wadanda jam iyyar APC ta yi sasanci akan su, su rike sabbin shugabannin jam iyyar APC ta jahar katsina.
Wasu yan tawaye biyu sun bulla.inda dayan su ya sawo fom na neman takarar shugaban jam iyya.
Daya kuma na neman takarar organizing saktare na jaha.
Takardun da jaridun katsina city news suka gani.wani mai suna Gide yaro daga kofar fada sabuwar kasa karamar hukumar kafur ya sayo fom na neman takarar shugaban jam iyya a jaha
Mun ga takardar shaidar biyan kudin fom a banki,da kuma fom din Wanda suka samo daga sakatariyar jam iyyar ta kasa dake Abuja.
Fom na biyu da jaridar nan ta gani shine na yahaya nuhu daga mahuta ta karamar hukumar dandume. Wanda shima akwai takardar banki da aka biya da fom din da suka samo daga sakatariyar jam iyyar dake Abuja.
Binciken mu a hedkwatar APC abuja ya tabbatar mana fom din na gaske ne.kuma a can aka basu,bayan sun biya kudin kamar yadda tsarin jam iyyar da kuma doka ya tanada.
Mahuta da gide sunyi takakkiya har ofishin jaridun katsina city news inda suka bayyana ma editocin jaridun cewa ,sun sayi fom .kuma suna sa ran su shiga zaben da za ayi ranar asabar 16/10/2021.
Sun fada ma jaridun katsina city news cewa, sun sanar da kwamitin shirya zaben na gobe cewa ,suna cikin takara.sun kuma sanar da wakilan da aka turo su gudanar da zaben daga Abuja .
Wakilan jaridun katsina city news sunyi kokarin ganin sunyi magana da kwamitin zaben na jaha da kuma na tarayya sun kasa samun su.
Katsina city news
Www.katsinacitynews.com
Jaridar taskar labarai
Www.jaridartaskarlabarai.com
The links news
Www.thelinksnews.com
07043777779 081377777245
Katsinaoffice@yahoo.com

KATSINA CITY NEWShttps://www.katsinacitynews.com
Danjuma Katsina, Dan Jarida, Manazarci, Marubuci, Mamallakin Jaridun KATSINA CITY NEWS, JARIDAR TASKAR LABARAI, THE LINKS NEWS, a karkashin Kamfanin MATASA MEDIA LINKS NIGERIAN LTD

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

WATA SABUWA: Kotu a jihar Gombe ta ci saurayi tarar Miliyan 2.6 saboda yaki auren budurwar sa

Daga: Yushau Garba Shanga Wata kotun majistiret da ke da zama a Kumo fadar ƙaramar hukumar Akko a jihar Gombe ta yanke wa wani matashi...

Rundunar Yansanda Ta Jihar Katsina Ta Chafke Daya Daga Cikin Yan Bindiga Da Suka Hallaka Hakimin Yantumaki.

Rundunar Yansanda ta Jihar Katsina ta samu nasarar chafke daya daga cikin Yan Bindiga da suka hallaka Tsohon Hakimin Yantumaki Marigayi Abubakar Atiku Maidabino,mai...

THE DUALIZATION OF THE IBADAN – ILORIN EXPRESSWAY AND SECTION II OF THE OYO – OGBOMOSO ROAD BY THE BUHARI ADMINISTRATION IS ALMOST DONE!

#PositiveFactsNG In staying true to its passionate commitment to developing Nigeria's infrastructure, do you know that the dualization of the Ibadan - Ilorin Expressway as...

THE APAPA – OSHODI – OWORONSHOKI EXPRESSWAY IS SET FOR COMPLETION AND COMMISSIONING!

https://www.facebook.com/Do-You-Know-NG-101788642037662/ THE APAPA - OSHODI - OWORONSHOKI EXPRESSWAY IS SET FOR COMPLETION AND COMMISSIONING! #PositiveFactsNG Do you know that the reconstruction project of the Apapa - Oshodi...

Kungiyar Mafarauta ta Najeriya HCN ta Karrama Mataimakiyar shugaba ta ƙasa

Kungiyar Mafarauta ta Najeriya HCN ta Karrama Mataimakiyar shugaba ta ƙasa Zaharaddeen Ishaq Abubakar @Katsina City News 6/12/2021 Kungiyar Mafarauta ta Najeriya, wato Hunters Council of...