Zaben Ondo: Gwamna Akeredolu ya lashe kananan hukumomi 9 daga cikin 12 da INEC ta bayyana sakamakon su.
Gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu ya lashe zabe a kananan hukumomi 9 daga cikin 12 da hukumar zabe me zaman, INEC ta fadi sakamakonsu daga zaben da aka gudanar Jiya, Asabar.
Gwamnan ya samu nasara mafi girma a daga karamar hukukar da ya fito, watau Owo inda ya samu kuri’u 35.957, yayin da kuma abokin takararsa na PDP ya samu kuri’u 5,311, dan takarar ZLP kuwa ya samu kuri’u 408 ne daga karamar hukumar.
Ga yanda sakamakon yake:
Akoko North-West – APC: 15, 809 – PDP: 10,320
Akoko North-East – APC: 16,572 – PDP: 8,380
Akoko South-East – APC: 9,419 – PDP: 4,003
Akoko South-West – APC: 21,232 – PDP: 15,055
Ifedore – PDP: 11,852 – APC:9,350
Akure North – PDP: 12,263 – APC: 9,546
Ile-Oluji/Okeigbo – APC: 13,278 – PDP: 9,231
Akure South – PDP: 47,627 – APC: 17,277
Owo – APC: 35,957 – PDP: 5,311
Idanre – APC: 11,286 – PDP: 7,499
Ondo East – APC: 6,485 – PDP: 4,049
Irele – APC: 12,643 – PDP: 5,904