Daga Bishir Suleiman @Katsina City News
Duk tirka-tirkar da ake na fitar da yantakara a jam’iyya mai mulki ta APC a jihar Katsina, babu zaben da aka kagauta da ji da Gani tamkar zaben fitar da gwani na yantakarar Gwamna da zai gudana a gobe Alhamis 26/5/2022 idan Allah ya kai mu.
Zabe ne da za a iya kira mafi girma da tarihi a jihar katsina, domin kowa ce shiya cikin shiyoyin dan majalissar Dattawa na jihar katsina, an samu zakakurin Dantakarar Gwamna da ya fito, kuma har yau an kasa samu daidaito na janyarwar wasu yantakarar su bar wa wasu, kamar yadda aka gani a sakamakon gayyatar da Gwamna Masari ya yi masu a gidansa, amma yantakarar biyu cikin taran basu samu halarta ba.
Faruk Lawal Jobe na daga cikin wadanda bai samu halarta ba, yana yankinsa don kara neman amincewar masu zaben fitar da gwani.
Al’umma jihar katsina suna ganin akala tafiyar da Katsina, a Jam’iyyar APC a matakin da ake yanzu na a hannun daligate, inda suke kira a gare su da su yi Allah su dubi halin da katsina take ciki, su zabar ma ta Dantakarar masanin jiya da yau da sarrafa taro ya zama naira wanda aka dade ana damawa da shi a cikin gwamnatin nan, tun daga SA har ya zuwa Kwamishina, ya kuma samu shiga aikace-aikace da dama da gwamnatin Katsina ta gudanar, wasu ya jagoranta wasu ya zama memba, kuma da daya fito wa Jam’iyyar tasu ta APC takarar Gwamna daga shiyar Funtua, wato, Alhaji Faruk Lawal Jobe.
Takarar shi ne kadai daga yankin Funtua, duba da cewar shiryar Katsina na da yantakara guda shida ko a cikin karamar hukumar katsina akwai guda uku, Dutsinma, Charanci da Danmusa na da mutum guda guda.
Ita ma shiyar Daura, akwai a karamar hukumar Daura da kuma Kankia. Abin Jira a gani dai Daligate za su duba diyauci ba tare da sun sayar da jam’iyyar ta APC Sun duba yanke da bai da turmotsatun yantakarar Gwamnan.
Fatan mu dai Allah ya Ida nufin Alhaji Faruk Lawal Jobe, 2023.