Rahotanni sun bayyana cewa, tsohon shugaban ƙasa na mulkin Soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangida IBB, baya goyon bayan Atiku Abubakar ko Bola Tinubu su zama shugaban ƙasa a 2023.

Rahoton yace dalilinsa shine a shekarar 2023, dukansu zasu shiga shekaru 70.

IBB bai fito ƙarara ya kira sunayen Atiku da Tinubu ba, amma a fakaice, yace kamata yayi ƴan Najeriya su mayar da hankulansu kan ƴan shekaru 60 wajan zaɓar shugaban ƙasa a 2023.

Nan da shekarar 2023, Atiku Abubakar zai cika shekaru 77 yayin da Bola Ahmad Tinubu zai cika shekara 70.

IBB wanda shima nan da 17 ga watan Augusta zai cika shekaru 80, ya bayyana cewa, ɗan shekaru 60 zai iya shugabancin Najeriya yanda ya kamata.

IBB ya bayyana haka ne a hirarsa da Arise News inda ya bayyana cewa dalilin da yasa Najeriya ta kasa cimma ci gaban da dattawan da suka kafata shi ne rashin kishin ƙasa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here