Daga El-Zaharadeen Umar, Katsina

Hon. Sani Aliyu Ɗanlami ɗaya ne daga cikin makusantan gwamna Aminu Bello Masari sannan shi ya riƙe kwamishinan walwala da jin daɗi da wassani na jihar Katsina wanda ya ajiye aikinsa cikin wannan satin domin fuskantar takarar kujerar majalisar tarayya a zaɓe mai zuwa.

Haka kuma daga cikin mutanen ƙalilan da aka matsawa lamba da su fito takarar a wannan kakar zaɓe wanda kuma ya amsa kiran da al’ummar ƙaramar hukumar Katsina suke yi masa domin ya yi takarar ɗan majalisar tarayya a zaɓe mai zuwa.

A wata hira ta musamman da ya gudanar da wasu keɓaɓun kafafen yada labarai jim kaɗan mika takardar ajiye aikinsa na kwamishina ya yi ƙarin haske dangane da fitowar sa takarar da kuma yadda jama’a suke yi masa kyakyawan zato.

Lokacin wannan tattaunawa da kafafen yaɗa labarai Hon. Sani Aliyu Ɗanlami ya yi bayanai masu yawan gaske kuma lallai ya nuna cewa shi ba ɗan dagajin siyasa ba ne, yasan abinda yake a siyasa.

Daga yadda yake bayani kawai ya ishe mai karatu fahimtar wanene Hon. Sani Aliyu Ɗanlami, sannan tsari da kuma masaniyar da yake da ita akan sha’anin siyasa zai baka amsar cewa lallai ba haka kawai jama’a suka matsa masa sai ya fito takara ba.

To amma, duk ba wannan ba abinda nake so jama’a su sani ba, Hon Sani Aliyu Ɗanlami ya yi wasu batutuwa da suke buƙatar nutsuwa a fahimce su da kyau.

Ni kaina da nake wannan rubutu na riga na gama sakankancewa Hon. Sani Aliyu Ɗanlami masanin siyasa ne da halayyar jama’a musamman na ƙaramar hukumar Katsina.

Buɗe bakinsa ke da wuce ya ce “idan Allah mai kowa mai komi, mai bada mulki ga wanda ya so, a lokacin da ya so, ya bani nasarar wannan kujera ta ɗan majalisar tarayya mai wakiltar Katsina ta tsakiya, to ina da abubuwa guda goma da zan tabbatar sun wakana kuma sun wanzu a wannan lokaci, insha’Allahu” inji shi.

Na farko, jama’ar da suka jajirce cewa zan iya wannan aiki tunda na taɓa yi, ba zan taɓa fifita buƙatuna fiye da na su ba, haka kuma ba zan taɓa raina su ba ku juya ba su baya ba, na tabbatar da sun san haka shi yasa suka dage sai ni, zan yi iya koƙari na wajan ganin mun daidaita sha’anin siyasar Katsina ta tsakiya da tashi halin ni ‘ya su a yanzu.

Abu na biyu kuma mai matuƙar muhimmanci shi ne, jam’iyyata ta APC wanda insha’Allahu da ita ce zamu kai ga nasara, mutunta Jami’yyar da shuwaganinta ya zama dole domin Kadda wata rana a rubuta sunana a jerin waɗanda suka yi wa jam’iyya butulci.

Abu na uku, shi ne, duk lokacin da wata buƙata ta jama’ar da nake yi wa wakilci ta ta so, insha’Allahu zan kasance a sahun gaba wajan kai kokon bararmu wajan da ya kamata, sannan in tabbatar an samu nasara.

Abu na huɗu, shi ne ba wai alfahari ba, duk wanda ya sanni, ya sanni da cewa bani da tarihin raina jama’ar ko guje masu, wannan damar zan yi amfani da ita wajan jin koken al’ummar da nake wakilta in Allah ya bani nasara.

Abu na biyar shi ne, zan yi amfani da sanaya wajan nemawa jama’a dama musamman matasa da mata abinda za su yi alfahari da nii ko bayan ba raina, ba sai na faɗa ba abubuwan da na ɗan yi a bayan sun isa misali.

Abu na shida shi ne, neman goyan bayan jama’a ta ta ƙaramar hukumar Katsina wajan ganin na sauke nauyin da kuka ɗora mani na shugabanci.

Abu na bakwai, insha’Allahu ba cika baki ba, zan kasance ɗan majalisar da za a daɗe ba ayi irin sa ba wajan tafiyar da sha’anin jama’a dama an ce wanda Allah ya ba wata baiwa wata rana zata tsairatar da shi, abin nufi anan shi ne, ina da masaniyar duk wainar da ake toyawa a majalisar wakilai ta tarayyar wannan zai bani dama wajan yin abinda ya kamata.

Abu na takwas, shi ne ina mai baku tabbacin ba zan taɓa zama kurma a majalisar wakilai ta tarayyar ba, bakin gwargwado ina da sani hakkin jama’a a kaina saboda haka zan fitar da ku kunya in Allah ya amince.

Abu na tara, shi ne, duk wata huɗɗar siyasa da zan yi, to insha’Allahu zamu yi ta cikin tsari da bin doka da oda, haka kuwa shi zai nuna dattaku da yakana da sanin girman jama’a waɗanda su ne suka nemeni in fito wannan takara.

Abu na goma kuma na karshe shi ne, tawakali ga Allah, wanann takara da jama’a ke son in yi, na dade ina tuntubar ‘yan uwa abokan arziki da masoya wanda daga karshe na miƙa komi zuwa ga Allah ya yi mani zaɓi tare da mutanen Katsina ta tsakiya, inda a karshe dai na amsa kira zan yi wannan takara, sai dai fatan Allah ya yi mana jagora

Bayan gama wannan jawabi na shi, sai kawai na ji a yanzu bani da wata tambaya sai nan gaba idan an fara wannan sha’ani domin an ce ka saurarawa mutumin da yake ganin girman na ga gare shi, ka kyale wanda baya juyawa na tare da shi baya, ka taimakawa wanda yake son taimakon jama’a, idan ba haka ba, to za a yi babu Kai. (Mai Raba Alheri Muka Kawo)

Taken dai shi ne, ga Allah Muka dogara kuma gareshi muke nema.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here