Home Sashen Hausa Za'aima sabuwar Rundunar SWAT gwajin ƙwaƙwalwa

Za’aima sabuwar Rundunar SWAT gwajin ƙwaƙwalwa

 

SWAT: Babban Sifeton ‘yan sandan Najeriya ya kafa rundunar da za ta maye gurbin SARS

Sufeton ƴan sandan Najeriya

Babban sifeton rundunar ‘yan sandan Najeriya ya kafa rundunar da za ta cike giɓin da rundunar SARS da ke yaƙi da fashi da makami ta bari.

Sunan rundunar Special Weapons and Tactics (SWAT) a turance.

Sanawar da Frank Mba, mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan ƙasar ya fitar ranar Talata, ta ce Babban sifeton ‘yan sandan Mohammed Adamu ya ɗauki matakin kafa rundunar ce domin yin aikin da SARS take gudanarwa kafin a rusa ta.

“Za a gudanar da gwajin lafiyar ƙwaƙwalwa da ta sauran jiki kan dakarun wannan sabuwar runduna domin ganin dacewarsu ta gudanar da aiki,” a cewar Mr Mba.

Ya ƙara da cewa a makon gobe ne dakarun rundunar za su soma samun horo kan ayyukan ‘yan sanda na musamman a sassan ƙasar daban-daban.

A yayin da dakarun rundunar daga rundunonin da ke Kudu Maso Gabashi da Kudu Maso Kudanci za su samu horo a Kwalejin Koyar da Yaki da Ta’addanci da ke Nonwa-Tai, jihar Rivers, su kuwa dakaru daga rundunonin Arewaci da Kudu Maso Yammaci za su samu nasu horon ne a Kwalejin Horas da ‘Yan sanda da ke Ende, jihar Nasarawa da takwararta da ke Ila-Orangun, jihar Osun, in ji sanarwar.

Wanne hali ‘yan sandan rundunar SARS da aka rushe ke ciki?

SARS
Bayanan hoto,Dakarun SARS da aka rusa za su nufi Abuja domin yi musu gwajin ƙwaƙwalwa

Kakakin rundunar ‘yan sandan ta Najeriya ya ƙara da cewa babban sifeton ‘yan sandan ƙasar ya bayar da umarni ga dukkan dakarun SARS da aka rushe su tafi hedikwatar rundunar da ke Abuja inda za a yi musu bayani sannan a gwada lafiyar ƙwaƙwalwarsu da ta lafiyar jikinsu.

“Ana sa ran yin gwajin kan dakarun ne domin kintsa su wajen samun ƙarin horo da wayar da kai kafin a sake tura su don gudanar da aikin ɗan sanda,” a cewar sanarwar.

A ƙarshen makon jiya ne Babban Sifeton ‘Yan Sandan Najeriya ya soke rundunar SARS bayan jerin zanga-zangar da aka ɗauki kwanaki ana yi a wasu jihohin ƙasar.

‘Yan ƙasar suna zargin rundunar ta SARS da azabtarwa da kisa ba bisa ƙa’ida ba da saɓa dokokin aiki.

Sai dai an ci gaba da zanga-zanga duk da rusa rundunar inda masu gangamin ke so a hukunta ‘yan sandan SARS da ake zargi da kisan mutanen da ba su ji ba ba su gani ba.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

Salihu Tanko Yakasai na hannunmu – DSS

Salihu Tanko Yakasai na hannunmu - DSS Rundunar 'yan sandan farin kaya ta DSS ta tabbatar da kama Salihu Tanko Yakasai, tsohon mai taimaka wa...

Ansako ɗaliban makarantar Kagara da aka sace

GSC Kagara: An sako mutum 41 da aka sace a makarantar Kagara ta Jihar Neja An sako ɗaliban makarantar Kagara da malamansu da ma'aikata guda...

PRESS RELEASE ; GANDUJE SACKS MEDIA AIDE

PRESS RELEASE GANDUJE SACKS MEDIA AIDE Governor Abdullahi Umar Ganduje of Kano state has relieved his Special Adviser on Media, Salihu Tanko Yakasai of his appointment...

KANO STATE POLICE COMMAND DIARY 26/02/2021

KANO STATE POLICE COMMAND DIARY 26/02/2021 7 DAYS ACHIEVEMENTS OF CP SAMA'ILA SHU'AIBU DIKKO, fsi IN KANO STATE ... As 9 Kidnapping Suspects, 8 Armed Robbery...

Bamu da Adalci, Dole ne mu cire batun Siyasa idan ba Haka ba Muna gidajenmu zamu Hallaka ~Inji Atiku Abubakar..

Bamu da Adalci, Dole ne mu cire batun Siyasa idan ba Haka ba Muna gidajenmu zamu Hallaka ~Inji Atiku Abubakar.. Tsohon mataimakin Shugaban Kasa Atiku...
%d bloggers like this: