Za a fara kamen mata masu bara a Kano

Gwamnatin Kano ta ce ta za ta fara kamen mata masu bara da kuma kwana a tituna a fadin Jihar.

Kwamishiniyar Harkokin Mata ta Jihar Kano, Zahra’u Mohammaed Umar ta ce gwamnatin Jihar ta dauki matakin ne don yaki da matan da ke baro gidajensu da garuruwansu musamman don yin bara a Kano inda suke kwana a karkashin gadoji da kan tituna da sunan bara.

A cewarta, hakan na daga cikin hanyoyin da ke jefa rayuwar mabaratan cikin mawuyacin hali musamman idan suka fada a hannun bata gari.

Don haka ta ce Jihar ba za ta lamunci bara ta zama barazana ga rayuwar mutane ba.

Ta ce hakan ne ya sa da zarar ta samu koken irin matan take ba su tallafin da za su fara sana’ar dogara da kansu.

Ta yi bayanin ne a cikin shirin ‘Barka da Hantsi’ na gidan rediyon Freedom, da ke Kano ranar Talata.

Hoto Daga: Vanguard News

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here