Za’a Zabtare Wani Kaso Daga Cikin Albashin Ma’aikata Da Kuma Ƴan siyasa Domin Taimaka Ma Ƴan kasuwa A Katsina…. Masari

Gwamnatin jihar Katsina ta bayyana aniyarta na cirar wani kaso daga cikin albashin ma’aikatan jahar domin cike gurbin asarar da gobarar da aka yi a babbar kasuwar Katsina ta janyo.

Gwamna Aminu Masari ne ya bayyana haka a yayin da ya ke amsar bayani daga Kwamitin da ya kafa domin binciken musabbabin gobarar da kuma yawan dukiyar da aka yi asara, wanda Kwamishinan ma’aikatar ayyuka da gidaje da kuma sufuri, Tasi’u Ɗanɗagoro ya jagoranta.

Masari wanda a ranar Larabar nan ya amshi sakamakon binciken da kwamitin yayi, ya ce kashi sama da 80 na dukiyar Katsina tana zuwa ne ga ma su riƙe da manyan muƙamai a gwamnatance da kuma ma’aikata, don haka ne ya yanke shawara a kan su ma su riƙe da manyan muƙaman gwamnati da ma’aikata da su bayar da gudunmuwarsu domin tallafa ma waɗanda gobarar ta shafa.

A ƙarshe duba ga irin dumbin matsalolin da jahar ke fuskanta na ƴan ta’adda da kuma asarar dukiyoyi da rayukan mutane, Masari yayi kira ga al’umma da su koma zuwa ga Allah domin tuba gare shi.

A cikin bayanin da Kwamitin yayi, ya bayyana zunzurutun kuɗi har sama da Naira Milyan Ɗari Tara 9 da Biyu 2 da aka yi a sararsu sakamakon gubarar.

Jakadiya Radio and Television JRTV

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here