Rahotanni sun bayyana cewa, ana shirin yiwa tsohon Shugaban hukumar yaki da rashawa da cin hanci, Ibrahim Magu karin mukami zuwa AIG.

Hakan na zuwa ne duk da yake Rahoton Kwamitin Ayo Salami ya bayyanashi a matsayin wanda ya aikata laifin rashawa lokacin yake rike da mukamin shugaban EFCC.

Saidai Rahoton da TheCable ta ruwaito yace, a cikin makonnan ne ake shirin yiwa Magu karin mukami.

Kwamitin Salami ya bada shawarar cire magu dannan a hukuntashi kan zarge-zargen da ya masa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here