Daga: Janadu Ahmadu Doro

Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta Bayyana kulle hanyar Dutsinma zuwa Ƙanƙara, da kuma Dutsinma zuwa garin Tsaskiya.

Kamar yadda rundunar ‘yan sandan ta bayyana za a rufe hanyoyin ne na Dan wani lokaci saboda zuwan shugaban ƙasa Muhammadu Buhari da zai ƙaddamar da Aikin Ruwan Dam din Zobe da ke Dutsin-Ma.

Rundunar ‘yan sandan na Sanar da Al’umma cewa Shugaba Buhari zai zo jihar Katsina a gobe alhamis don ƙaddamar da Aikin Ruwan Zobe Dam da kuma Sabuwar hanyar da aka gina ta Tsaskiya a cikin ƙaramar hukumar Safana ta jihar Katsina.

Don haka rundunar na Sanar da Jama’a cewa za ta kulle hanyar Dutsinma zuwa Kankara da Dutsinma har zuwa sabuwar hanyar Tsaskiya da duk wata hanya da za ta iya kai Mutum zuwa wajen ƙaddamar da wadannan ayyukan na Wani Ɗan lokaci.

Ana Sanar da jama’a musamman Direbobi, Makiyaya, Jama’ar Gari, Masu Babura da su ƙaurace wa wannan hanyoyin da aka ambata su yi amfani da wasu har zuwa lokacin kammala Bikin ƙaddamarwar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here