Gwamnatin Tarayya ta shirya tsaf, domin ƙaddamar da cibiyar samar da wutar Lantarki mai amfani da ƙarfin Iska mai ƙarfin megawat 10 a Lambar Rimi da ke Jihar Katsina nan da makonni takwas?

An faro aikin wannan Cibiyar ne a zamanin Marigayi Malam Ummaru Musa Yar’Adua yana Gwamnan Katsina a 2005 kafin Gwamnatin Tarayya ta amshe shi a 2007.

Aikin ya yi ta samun tafiyar hawainiya, kafin zuwan Gwamnatin Shugaba Buhari, dama bayan zuwan ta, ya zuwa yanzu dai aikin ya laƙume kudi Kimanin Naira Biliyan 4.4.

An daiyi ta sanya ranar cewa za’a ƙaddamar da wannan tashar amma anata kwangaba kwanbaya, abun jira anan shine muga Idan Allah ya kaimu Makonni Takwas din masu zuwa ko za’a ƙaddamar din kamar yadda aka yi Alkawari a wannan karon

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here