Gabanin Za6en Kananan Hukumomin Jihar Katsina, dan takarar gwamnan jihar katsina karkashin Inuwar jam’iyyar Adawa ta PDP, Salisu Yusuf Majigiri ya halarci yakin neman za6en Maza6un Dugoru ‘A’, Gallu, Sonkaya da kima Karau wadanda ke karamar Hukumar Mashi ta jihar katsina, domin yakin neman za6en Kananan hukumomin jihar wandda za a yi a ranar 11 ga afrelun nan.

A yayin gudanar da wannan yakin neman za6en, an yi zamiya ne a kowace hedikwata ta maza6un da aka je.

Yayin dukkan wadannan ziyararori, Majigiri ya yi kira da kuma sheda wa al’umma cewa yanzu lokaci ya yi da za su zo su tabbatar sun kawo karshen Mulkin Yunwa, Tsadar rayuwa, Talauci gami da Kunci da sauran wahalar rayuwa wanda a cewarsa gwamnatin APC ce ta je fa al’umma a cikinsu.

Salisu Yusuf Majigiri ya ƙara yin kira ga ƴa’ƴan al’umma da su mai da hankali sosai su kuma sa ido wajen ganin an yi sahihin zaɓe na adalci wajen kasawa da tsare ƙuri’unsu har sai an bayyanar da sakamako, tun daga rumfunan zaɓe zuwa wurin tattara sakamakon za6e na kowace maza6a, a nan take kuma su tsaya sai an bayyanar da Kansilan da ya ci za6e na kowace maza6a .

Yayin wannan yakin neman za6en, an kar6i daruruwan al’umma daga garuruwa daban-daban na wadannan maza6u wadanda suka fito daga jam’iyyar APC zuwa jam’iyyar PDP, inda Jagororin nasu suka bayyana irin gazawa da Jam’iyyar APC katsina ta yi da kuma mummunan halin da ta jefa al’umma a ciki, a cewarsu.

Sun kara da cewa; “A saboda haka muka ga kara mu bar ta mu koma zuwa Jam’iyyar PDP, domin muna da yakinin Mulkin PDP yafi na APC sau 100” – In ji su.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here