Advert
Home Sashen Hausa ZA MU ILMANTAR DA JAMA'A DOMIN CETO JIHARMU

ZA MU ILMANTAR DA JAMA’A DOMIN CETO JIHARMU

Kungiyar hadin kan katsinawa da daurawa

Daga kamilu lawal
@ katsina city news
Shugaban kungiyar hadin kan katsinawa da daurawa Dakta Magaji Dan sarai ya bukaci al’ummar jihar masu kishin al’umma su shigo siyasa domin bada gudummuwar su wajen fitar da jihar daga kalubalen da take ciki
Dakta magaji dan sarai ya bukaci hakan ne a Katsina lokacin da yake ganawa da manema labarai
Kamar yadda ya bayyana duba da halin da jihar take ciki a yanzu bai kamata mutanan kirki su rika dari dari da shiga harkokin siyasa ba saboda tsoron dabi’un da suke ganin harkar siyasa na dauke da su ba
Yace madamar zasu shiga da kyakkyawar manufa da Imani da Allah to Allah zai basu nasara
Dakta magaji dansarai ya bayyana cewa sanin kowa ne jihar Katsina na da kwararru da ake bukata a kowane fanni domin fitar da jihar daga kalubalen da ta samu kanta
Ya bukaci jam’iyyun siyasa da sauran masu ruwa da tsaki su bada dama ga Ingantattun mutane masu kishin al’umma a kowane Irin wakilci na jagoranci musamman a yanzu da ake shirye shiryen gudanar da zabukan cikin gida na shugabannin jam’iyyun
Ya jaddada kudurin kungiyar na cigaba da Ilmantar da al’ummar jihar Katsina domin ceto su daga halin da suke ciki
Yana mai cewa
“bai kamata mutane masu kima da martaba kamar yan jihar Katsina su kauda Idanuwansu game da yadda abubuwa ke tafiya ba,” cewar shugaban kungiyar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

NAF begins inquiry into alleged killings of civilians by Airforce pilot

The Nigerian Airforce has begun investigations into the alleged killing of civilians in Kamadougou Yobe State by an Airforce pilot. In a statement on Friday...

Yanzu haka cikin daren nan ‘yan bindiga sun afkawa garin Tangaza

LABARAI DA DUMI-DUMIN SU! Yanzu haka cikin daren nan 'yan bindiga sun afkawa garin Tangaza Labarai da muke samu sun tabbatar da cewa yanzu haka cikin...

Siyasa: PDP tayi watsi da tsagin Aminu Wali ta rungumi Kwankwaso

Siyasa: PDP tayi watsi da tsagin Aminu Wali ta rungumi Kwankwaso Babbar jam'iyyar adawa ta PDP ta sanya ranar gudanar da zaben sabbin shugabanninta na...

Abdulaziz Ganduje ya kai karar mahaifiyarsa Gwaggo EFCC kan batun almundahana

Babban dan Gwamnan Kano, Abdulaziz Ganduje ya maka mahaifiyarsa Hafsat Ganduje gaban hukumar yakibda yiwa tattalin arziki zagon kasa ta EFCC akan zargin da...

Barawon Motar Gwamnati Ya Shiga Hannu A Katsina

Barawon Motar Gwamnati Ya Shiga Hannu A Katsina. Rundunar Yan Sanda ta Jihar Katsina ta samu nasarar chafke wani mai suna Hayatu Bishir da ake...
%d bloggers like this: