Ministan Sufurin Najeriya Mista Rotimi Amaechi, Dantakarar Shugaban ƙasar Najeriya

Ministan Sufuri na Najeriya, Rt Hon Rotimi Amaechi ya kawo ziyarar aiki da gaisuwa a jihar Katsina

Sarkin Katsina Alhaji Abdulmumini Kabir Usman CFR

Ministan Sufuri kuma tsohon Gwamnan jihar Ribas, Rt Hon Rotimi Amaechi ya kawo ziyarar wuni daya a jihar Katsina.

Dalilan ziyarar kamar yadda ya bayyana sun hada da duba ayyukan da ma’aikatar sa ke kula da su na ginin Jami’ar Kimiyyar hanyoyi ta garin Daura, gaisuwa ga Sarkin Katsina bisa rasuwar kanin sa, Sarkin Sullubawan Katsina Hakimin Kaita da kuma sanar da sarakunan Katsina da Daura da Gwamnan jihar Katsina aniyar sa ta tsayawa takarar shugabancin kasa.

Tun da farko dai tsohon Gwamnan Ribas din ya duba aikin ginin Jami’ar ta garin Daura inda ya yaba da yadda aikin ke tafiya tare da yaba wa kamfanin da ke yin aikin.

Haka zalika Minista Amaechi din ya kuma sanar da cewa Jami’ar za ta fara aiki ne a cikin watan Satumba mai zuwa.

Daga nan Ministan wanda kuma ke rike da sarautar Dan Amanar Daura ya je fadar sarkin Daura inda ya kai masa ziyarar ban girma tare da sanar da shi kudurin sa na tsayawa takarar shugaban kasa a zaben 2023 dake tafe.

Sarkin Daura a jawabin sa ya yabawa Ministan bisa yadda ya ce ya mutunta kasar Daura da mutanen ta musamman wurin Assasa ayyukan more rayuwa.

Daga nan kuma sai ya tabbatar masa da dukkan goyon bayan da yake bukata domin samun nasarar sa.

Tawagar Dan Amanar Daura, daga nan sai ta wuce fadar Sarkin Katsina inda a nan ma ya yi ma Sarkin na Katsina ta’aziyyar rasuwar kanin sa tare da shaida masa aniyarsa ta yin takarar shugabancin kasar Najeriya a zaben 2023 dake tafe.

A nan ma Sarkin ya yabawa Ministan bisa ayyukan raya kasa da ya kawo ma jihar da kuma yadda ya rike ma’aikatar sa da amana da kwarewa. Kuma Sarkin ya sha alwashin yi masa Addu’a don cimma gurinsa na shugabancin ƙasar da yake nema.

Daga karshe tawagar ta Ministan ta je wurin Gwamnan jihar Katsina, Alhaji Aminu Bello Masari a fadar gwamnatin jihar inda Ministan ya sanar da Gwamnan aniyar sa ta tsayawa takarar shugabancin Najeriya.

Gwamna Masari a na shi jawabin ya ba Ministan tabbacin goyon baya da kuma shawarwari inda duk ta kama.

Tawagar Dan Amanar na Daura da suka rako shi jihar Katsina ta hada da mai masaukin baki, kuma mai neman takarar Kujerar Gwamnan jihar Katsina, Sanata Sadiq Yar’adua, Sanata Ndume daga jihar Borno, tsohon kakakin majalisar jihar Sokoto, manyan ‘yan siyasa daga Kudancin kasarnan jami’an tsaro da ‘yanjarida.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here