Ministan Shari’a na Najeriya Abubakar Malami ya ce zai goge sashe na 84(12) na Dokar Zaɓe ta 2022 kamar yadda Babbar Kotun Tarayya ta umarce shi.

Wata sanarwa da ofishin ministan ya fitar a yammacin yau Juma’a ta ce za a buga kundin dokar ɗauke da gyaran da kotun ta yi.

A yau Juma’a ne dai kotun da ke zamanta a Umuahia na Jihar Abiya ta umarci Malami ya goge sashen da ya hana masu riƙe da muƙaman siyasa jefa ƙuria’a ko tsayawa takara a zaɓukan cikin jam’iyyu saboda ya ci karo da sashe na 287 na kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999.

Sashen na 287 ya tanadi cewa duk wani mai muƙamin siyasa ba zai iya shiga harkokin zaɓe ba har sai ya sauka daga muƙaminsa kwana 30 kafin ranar jefa ƙuri’a.

A ƙarshen watan Fabarairu ne Shugaba Muhammadu Buhari ya saka wa sabuwar dokar zaɓen hannu, yana mai kiran ‘yan majalisa da su soke sashen, amma sai suka ƙi yin hakan.

Hukunncin kotun ya biyo bayan wata ƙara ce da wani lauya ya shigar yana neman kotun ta fayyace dokar da za a bi tsakanin ta zaɓe ko kuma ta kundin mulki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here