Ministan Harkokin Sufuri na Ƙasa, Rotimi Amaechi ya baiyana cewa Gwamnatin Tariya na shirin ƙaro jiragen ƙasa guda 16 ta sanya su a hanyar layin dogo na Legas-Ibadan.

Amaechi ya baiyana hakan ne a wani shiri mai taken ‘ Hard Copy’ a gidan talabijin na Channels Television a ranar Asabar.

A cewar sa, ƙaro jiragen zai ƙara bunƙasa kuɗaɗen shiga ga gwamnati ta wannan ɓangaren na ƙasa.

Ya ƙara da cewa a yanzu haka, jigilar jirgin ƙasa a layin dogo na Abuja-Kaduna na samar da Naira miliyan 300 na kuɗin shiga a kowanne wata.

Ya kuma baiyana cewa gwamnatin Nijeriya ta fara biyan bashin da ta ciyo domin samar da jiragen ƙasa, inda ya baiyana yaƙinin cewa gwamnati za ta biya kudin baki ɗaya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here