Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayar da umarnin a sassauta tutar ƙasar a dukkan gine-ginen gwamnati yayin da ake ci gaba da makokin rasuwar shugaban sojan ƙasa Janar Ibrahim Attahiru da wasu sojoji 10.

Kazalika, shugaban ya bai wa dakarun rundunar sojojin ƙasar hutun aiki a yau Litinin. Sannan umarnin zai fara aiki ne daga Litinin zuwa Laraba.

A ranar Asabar ne aka yi jana’izar Babban Hafsan Sojan Ƙasa Laftanal Janar Ibrahim Attahiru tare da wasu sojoiji 10 bayan sun rasu a hatsarin jirgin sama a kusa da filin jirgin sama na JIhar Kaduna da ke arewacin ƙasar.

An binne su a Maƙabarta ta Ƙasa da ke Abuja.

Guda shida daga cikinsu Musulmai ne da aka yi wa sallah a Babban Masallacin Abuja, yayin da aka yi wa Kiristoci jana’iza a Babbar Cocin Abuja.

Buhari ya bayyana kaɗuwa da rasuwar Janar Attahiru sannan ya umarci a gudanar da bincike game da abin da ya haddasa hatsarin jirgin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here