Rahotanni daga Jihar Kaduna na bayyana cewar Gwamnatin jihar ta ce za ta sake yi wa malaman makarantun frimare gwajin sanin makaman aiki a yunkurinta na tabbatar da samar da ilimi mai inganci a makarantun faɗin Jihar.

Malam Mohammed Mubarak, Mamba na dindindin, Sashin Sanya Ido Kan Ayyuka, Hukumar Kula da Makarantun Frimare na jihar Kaduna ne ya sanar da hakan yayin tattauna da manema labarai a Kaduna a ranar Laraba.

Mubarak ya ce gwamnatin jihar, a 2017 ta sallami kimanin malamai 22,000 da ba su cancanta ba daga makarantun frimari domin sun fadi jarrabawar gwajin sanin makaman aiki warwars.

Ya ƙara da cewar dole ta sa aka dauki matakin mai wahala, yana mai cewa gwamnati ta maye gurbin malaman da ta sallama da wasu 25,000 da suka cancanta da ake yi wa tankade da reraya.

Ya yi bayanin cewa a yanzu hukumar na shirin yin wani gwajin sanin makaman aiki ga malaman frimari da nufin tabbatar da samar da ilimi mai nagarta a makarantun na frimare. Ya ce: “Kuma a halin yanzu muna kashe Naira miliyan 341 a kan bawa malaman horaswa domin kwarewa kan aiki da tallafi daga hukumar ilimi bai daya.

“Hakan ya dace da tsarin gwamnatin jihar na tabbatar da samar da ilimi mai nagarta da koyarwa a dukkan makarantun jihar.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here