Za a fara aikin jirgin kasa daga Ibadan zuwa Kano

FMOT

Ma’aikatar sufuri ta Najeriya ta ce za ta kaddamar da aikin layin dogo da zai taso daga Ibadan ta jihar Oyo zuwa jihar Kano da ke arewwacin kasar.

Ma’aikatar ta bayyana hakan ce cikin jerin sakonnin Twitter da ta wallafa a shafinta.

Cikin fatan da gwamnati mai ci take da shi na hade duka bangarorin kasar ne da layin dogo yanzu za ta kaddamar da aikin jirgin kasan da zai taso daga Ibadan zuwa Kano.

Ministan Sufuri na kasar Amaechi ya ce gwamnatin Najeriya ta bayar da nata kason, yanzu ana jiran bankin China-Exim ya gabatar na nasa sannan a fara aiki gadan-gadan.

Ministan ya ce ba za a sauya yadda aka tsara yin wannan layin dogon ba, kamar yadda aka sauya wanda aka yi tsakanin Legas da Ibadan.

Social embed from twitter

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here