Zaɓen 2023: Ɗan Sadau ya yima Shuwagabannin Jam’iyyar PDP na Katsina ta tsakiya Shatara ta Arziki

Hon. Lawal Ɗansadau tsohon Dantakarar majalisar tarayya a ƙarkashin Jam’iyyar APC wanda yayi ƙaura daga jami’iyya zuwa APCn zuwa Jam’iyyar PDP ya gana da Chiyamomin Jam’iyyar ta PDP a mazabun Katsina ta tsaki su 11, a yunƙurin sa na neman tsayawa takarar sanata.

Dan sadau ya gana da Dukkanin shuwagabannin a Offishin na PDP na karamar hukumar Katsina inda ya jaddada aniyarsa sa ta tsayawa takara, sana ya nemi hadin kansu da goyon baya.

A watan da ya gabata ne Hon Dansadau ya fice daga jam’iyyar sa ta APC zuwa Babbar jam’iyyar Adawta PDP, a cewarsa ya gamsu da Manufofin jam’iyya da aka ginda akan tsari da adalci, kuma ya shigo jam’iyyar ne da shi da magoya bayansa domin rufawa Jam’iyyar baya don samun Nasara a kakar zaɓe mai zuwa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here