Daga Shuaibu Abdullahi

Rahotanni sun tabbatar da cewar Jam’iyyar adawa ta PDP ce tayi nasara a mazabar da Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasiru Elrufai yake kaɗa Kuri’a.

A lokacin da yake bayyana sakamakon zaben baturen zaben Muhammad Sani, ya ce jam’iyyar Apc ta sami kuri’u 62 yayin da Jam’iyyar adawa tayi nasara da kuri’u 86 daga cikin kuri’u 159 da aka kaɗa a mazabar Unguwar sarki a bangaren zaben Ciyaman.

Kazalika a zaben Kansiloli ma Jam’iyyar PDP mai adawa ce tayi nasara da kuri’u 100 yayin da jam’iyyar Apc ta sami kuri’u 53 daga cikin kuri’u 162 da aka jefa a mazabar.

Kawo yanzu baa kammala tattara bayanan zabukan zabukan ƙananan hukumomin ba kafin daga bisani a fadi sakamako.

Da yammacin yau shima Gwamnan Jihar Kaduna ya ƙada kuri’ar sa a mazabar tasa dake Unguwar Sarki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here