Janar Tukur Yusuf Buratai, babban hafsan rundunar soji ya daurawa manyan sojoji 39 damarar kara girma zuwa manjo janaral

– A jawabin da ya gabatar a wurin, Buratai ya ce shugabancin rundunar soji ta na sane da cewa wasu ‘yan siyasa na son ingiza manyan sojoji

– Buratai ya ce dimokradiyya ta zo kenan, ta zauna daram, an wuce lokacin da sojoji za su ke katsalandan cikin dimokradiyya

Babban hafsan rundunar sojoji, Janar Tukur Yusuf Buratai, ya yi gargadi a kan juyin mulki tare da jaddada cewa rundunar soji ba zata lamunci duk wani yunkuri na kawo hargitsi da zai lalata tsarin dimokuraɗiyyar ba.

Buratai ya bayyana hakan ne ranar Juma’a yayin da ya ke gabatar da jawabi bayan ya kammala daura damarar kara girma ga sabbin manyan sojoji 39 da aka karawa girma zuwa mukamin manjo janaral, kamar yadda Vanguard ta wallafa.

“Dimokradiyya ta zo kenan, ta zauna daram; har abada. Ba zamu yarda da duk wani yunkurin kawo hargitsi ba. Lokacin da sojoji za su ke tsoma baki a harkokin siyasa ya wuce, hakan ba zai kai mu ko ina ba. An wuce lokacin,” a cewarsa.

Buratai ya bayyana cewa shugabancin rundunar soji ya na sane da cewa wasu ‘yan siyasa su na son ingiza wasu manyan sojoji, amma, a cewarsa, ya yarda da tarbiyar sabbin manyan sojojin da suka samu karin girma.

“Kar ku kulla hulda da ‘yan siyasa. Kar ku nemi wani mukami ko alfarma daga wurin ‘yan siyasa, idan ku na bukatar alfarma ku nema a wurin shugaban rundunar soji, shi kuma alfarmarsa ta na samuwa ne ta hanyar aiki tukuru da jajircewa da biyayya,” a cewarsa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here