Advert
Home Sashen Hausa Yunƙurin Gwamnatin jihar Katsina na samar da Asibitin koyarwa (Teaching Hospital) ya...

Yunƙurin Gwamnatin jihar Katsina na samar da Asibitin koyarwa (Teaching Hospital) ya tabbata.

Daga Abdulhadi Ahamd Bawa

Muhimmancin da Gwamnatin jihar Katsina, karkashin jagorancin Gwamna Aminu Bello Masari, taba bangaren Ilimi da Lafiya, yasa tun cikin shekarar 2016 ta fara tuntubar Ma’aikatar lafiya ta Tarayya domin samun amincewar ta wajen amfani da Asibitin da aka fi sani da ta kwararru (FMC) domin Jami’ar Umaru Musa Yar’adua ta fara gudanar da digiri a fannin likitanci, amma sai wannan bukata bata samu shiga ba a wancan lokaci.

Duk da haka, Gwamnati bata fitar da rai ba, sai ta ci gaba da tuntubar tare bada karin dalilan da za su sa wannan bukata ta sami karɓuwa.

Alhamdu lillah, a yau Talata 8/12/2020, cikin ikon Allah, wannan haka ta cimma ruwa. Domin kuwa a yau Gwamnatin Tarayya, ta hannun Ma’aikatar lafiya ta Tarayy, ta amince da a daga darajar wannan Asibiti ta kwararru (Federal Medical Center) dake Katsina ya zuwa Asibitin koyarwa ta Tarayya domin Jami’ar Umaru Musa Yar’adua tayi amfani dashi wajen gudanar da Digiri a fannin likitanci (Medicine).

Wannan amincewa, tana cikin wata yarjejeniyar fahimtar juna da kuma aiki tare da Gwamnatin ta Tarayya a bangare daya da kuma Gwamnatin Jihar Katsina a daya bangaren suka sa ma hannu.

Gwamna Aminu Bello Masari shi yasa hannu a kan wannan yarjejeniya a madadin Gwamnatin Jihar Katsina a yayin da kuma Ministan Lafiya na kasa Dr Osagie Emmanuel Ehanire yasa hannu a madadin Gwamnatin Tarayya.

Daga cikin wadanda suka halarci taron sun hada da Ministan kasa a ma’aikatar lafiya Senator Olurunimbe Mamora da Babban Sakataren Ma’aikatar lafiya ta kasa Alhaji AbdulAzeez Abdullahi Mashi da Shugaban asibitin kwararru ta Katsina Dokta Suleiman Bello Muhammad da sauran daraktocin wannan ma’aikata.

Mai ba Gwamnan Jihar Katsina Shawara a bangaren ilimi mai zurfi Bashir Muhammad Ruwan Godiya da kuma Shugaban jami’ar Umaru Musa Yar’adua Farfesa Sanusi Mamman da kuma wasu manyan jami’an Gwamnatin jiha suka rufa wa Gwamnan baya.

Akwai kuma kungiyar Dattawan jihar Katsina, a karkashin jagorancin Alhaji Aliyu Balarabe Saulawa da taka muhimmiyar rawa wajen ganin an cimma wannan burin. Sanata Mamman Abubakar Danmusa da Alhaji Nalado Yusuf Daura suna cikin Dattawan da suka halarci wannan taro.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

An Naɗa Tsohon Shugaban Najeriya Goodluck Ebele Jonathan A Matsayin Shugaban Jami’ar Cavendish Ta Kasar Uganda (CUU)

An Naɗa Tsohon Shugaban Najeriya Goodluck Ebele Jonathan A Matsayin Shugaban Jami’ar Cavendish Ta Kasar Uganda (CUU) Mukamin na ‘Chancellor’ na jami’ar ta CUU ta...

“Shugaban Kasa Muhammadu Buhari Zai Gana da Dukkan Shuwagabannin Kananan Hukumomi a Kasar Nan”

LABARI DA DUMI-DUMIN SA! "Shugaban Kasa Muhammadu Buhari Zai Gana da Dukkan Shuwagabannin Kananan Hukumomi a Kasar Nan" Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai sanya labule da...

Shugaba Buhari Ya Baiwa Kwamitin Rage Talauci Umurnin Gaggauta Ceto Mutane Milyan Dari Daga Talauci A Najeriya

Shugaba Buhari Ya Baiwa Kwamitin Rage Talauci Umurnin Gaggauta Ceto Mutane Milyan Dari Daga Talauci A Najeriya A ranar Talata, 22 ga watan Yuni, 2021,...

Iran Carries Out 1st Remote Surgery with Home-Made Robot

Iran Carries Out 1st Remote Surgery with Home-Made Robot I am sharing this with Friends because the Western MainStream Media (MSM) will NEVER show you...
%d bloggers like this: