Yin sulhu da ƴan bindiga ragwanci ne- Babagana Munguno

Manjo Janar Babagana Monguno

Mai bai wa shugaban Najeriya shawara kan harkokin tsaro, Manjo Janar Babagana Munguno ya ce gwamnatin Buhari ba ta da ra’ayin tattaunawa da ƴan bindiga da ƴan ta’adda da suka addabi kasar.

A cewarsa, tattaunawa ko yin sulhu da su zai sa a yi wa gwamnati kallon raguwa ko kuma a ga kamar ta gaza. Ya ce a shirye gwamnatin ta ke ta yi amfani da ƙarfin tuwo a kan masu laifin.

A lokacin da ya ke jawabi a wani taro a fadar shugaban ƙasa a Abuja, Munguno ya ce gwamnati na iya bakin ƙoƙarinta wajen magance rashin tsaro. Ya ce suna bin abin daki-daki ne.

Haka kuma, ya ce gwamnati za ta yi amfani da duk wata hanya da take da shi ta kawo ƙarshen ƴan bindiga.

Ya ce idan ƴan ta’addar sun shirya magana da gwamnati, idan lokaci ya yi ana iya tattaunawa amma yanzu ba tattaunawar ce mafita ba.

Munguno ya ce bai ga dalilin da zai sa a zauna a yi sulhu da su ba.

“Shi ya sa nake son Gwamnan jihar kaduna, saboda matsayarsa ta ƙin tattaunawa da mutanen nan,” a cewarsa.

Ya ce Najeriya na da kayan aiki da jami’an tsaron da za a iya kawo ƙarshen ƴan bindiga.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here