Yawanci Musulmai Wayayyu Ne, Amma Pantami Baya Cikinsu – Obadiah Mai Lafiya

Tsohon Mataimakin Gwamnan babban bankin Najeriya, Obadiah Mailafiya ya bayyana cewa, Yawanci Musulmai wayayyu ne.

Yace amma Irin su Ministan Sadarwa da tattalin arzikin Zamani, Sheikh Isa Ali Pantami wanda a Salaf ne dake bin Ibn Taymiyya suna da matsala. Yace akidarsu irin ta su Hitler ce da Nazi wadda idan baka tare dasu basu dauke a matsayin mutum ba. Yace a karkashin irin koyarwarsu ne aka samu kungiyoyin Alqaeda, Al-Shabab da ISWAP.

Mai Lafiya ya kuma kara da cewa, babbar matsalar irin su Pantami masu haddar Qur’ani shine suna dauko abinda aka rubutashi da Larabci suce zasu fassara zuwa Hausa ko turanci wanda hakan abune me matukar wahala.

Ya bayyana hakane a hirar da aka yi dashi a jaridar Tribune da aka tattauna dashi akan abubuwa da yawa, wanda hutudole ya tsakuro muku wasu kadan daga ciki.

Mai Lafiya yace Pantami na nuna alamar son komawa Madina, yace suna maraba da hakan dan kuwa basa bukatar Irinshi a Najeriya. Yace Pantami ya kawowa Najeriya wani tsari washi na NIN kuma ana ta Shigo da Fulani daga kasashen waje ana musu rijistar wannan NIN din da ace sune suka fi yawa.

Yace akwai shirin Jihadi ne da ake yi a Arewa

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here