Yaushe Buhari zai dawo daga Landan?

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya shiga mako na Uku a Landan, batun da ya soma haifar da ce ce-ku ce kan ko zai tsawaita zamansa ne a can ganin babu wata sanarwa da aka fitar kawo yanzu kan dawowarsa ko akasin haka.

A ranar 30 ga watan Maris shugaban ya tafi Landan domin ‘duba lafiyarsa’ a cewar wata sanarwa da kakainsa Femi Adesina ya fitar.

Sanarwar ta kuma shaida cewa zai dawo Najeriya a mako na biyu na watan Afrilu. Sai dai har yanzu babu wani labari dangane da ranar dawowarsa.

Kuma kamar yada Jaridar Punch a Najeriya ta rawaito, Ministan yaɗa labarai da al’adu, Lai Mohammed yaƙi tsokaci kan ranar dawowar shugaban a taron majalisar zartwarwa da aka gudanar jiya Laraba a Abuja.

A makon da ya gabata ne kakakin shugaban Malam Garba Shehu ya fitar da wata wasika zuwa ga sarkin Jordan, yana mai cewa Buhari yaje Landan ne domin gajeren hutu.

Tafiyar Shugaban ta janyo ce ce-ku ce da zanga-zanga tsakanin masu adawa da magoya bayansa a Landan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here