Yau Buhari zai rattaba hannu kan kasafin kuɗin 2021

Nan gaba a yau Alhamis ne ake sa ran shugaba Muhammadu Buhari zai rattaba hannu kan dokar kasafin kudi ta shekarar 2021 da Majalisar Dokoki ta amince da shi.
Mai magana da yawun shugaban Garba Shehu ne ya tabbatar da hakan ga Daily Trust.
Wasu daga cikin waɗanda ake sa ran za su albarkaci sanya hannun sun haɗar da mataimakin shugaban ƙasa, Yemi Osinbajo, shugaban majalisar dattawa Ahmad Lawan, da kakakin majalisar wakilai Femi Gbajabiamila da wasu manyan yan majalisa.
Sannan akwai wasu mambobin Majalisar Zartarwa ta kasar (FEC) da ake sa ran za su halarci bikin sanya hannun, da suka hadar da Ministar Kudi Hajiya Zainab Ahmed, Karamin Ministan Kasafin Kudi da Tsare-Tsaren Clement Agba, da Gwamnan Babban Bankin Najeriya CBN) wato Godwin Emefiele, da Darakta Janar na Ofishin Kasafin Kudi Ben Akabueze da sauransu.