Advert
Home Sashen Hausa Yaro Bari Murna Karen ka Ya Kama Zaki....zaben exco a katsina 

Yaro Bari Murna Karen ka Ya Kama Zaki….zaben exco a katsina 

 

Daga Abdullahi I mahuta

Tsohon Dan majalisar a katsina

Bayan kammala zaben shugabannin jam’iyyar APC na matakin ‘ward’, na samu damar tattaunawa da wasu daga cikin abokai na guda biyu wadanda kuma dukkan su yanmajalisa ne.

Na farko na cikin damuwa saboda, acewar shi, an hana shi damar sanya yaran shi a cikin sababbin ‘exco’ na wards din karamar hukumar shi. Wanda rashin samun yaran shi a cikin exco, a ta shi fahimtar, zai hana ma shi damar sake cin zabe da ya ke Shirin tsayawa a 2023.

Na biyun kuma ya na ta murna da alfahari cewa shi duk yaran shi sun samu shiga cikin sababbin ‘exco’. Shi kuma, a ta shi fahimtar, wannan wani tabbaci ne na cewa ya gama samun nasara a zabe mai zuwa….

Sai na yi ma na farkon tambaya: “Amman Honourable, a lokacin da ka shigo harkar siyasa har ka tsaya takara kuma ka ci zabe a 2019, ai ka tarar da exco a wancan lokacin ko? ” Ya ce ma ni “haka ne”. Sai na tambaye shi ” to mutane nawa ne daga cikin exco na wancan lokacin wadanda kai ne ka sa sunayen su a matsayin exco?” Ya sake ba ni amsa da cewa shi bai ma taba sanin su ba sai a lokacin da ya shigo harkar siyasa a 2019. Na ce ma shi amman ka san cewa su ma exco din na wancan lokacin da su ka zabe ka, ka san da cewa wani ne daban ya rubuta sunayen su a bisa irin niyyar da ka ke da ita yanzu ko? Ya sake ce ma ni haka ne.

Sai na ce ma shi to ya aka yi ba su zabi wanda ya yi su ba, su ka zabe ka a wancan lokacin? Aboki na ya ce ma ni gaskiya shi ma abun ya ba shi mamaki, amman ya na ganin HUKUNCIN ALLAH ne kawai…

Na ce ma shi to Alhamdulillahi, tunda ka san hakan. Saboda haka Ina ba ka shawarar cewa ka saki exco ka Kama Allah.. Allah shi ke ba da mulki ga wanda ya so.

Na kalli dayan honourable din wanda ke murna cewa shi duk yaran shi sun samu shiga cikin sababbin ‘exco’, na ce ma shi kai kuma bari murna Karen ka ya kama Zaki. Domin shi exco ba amana ce da shi ba. Shi ya sa marigayi senator Kanti Bello ya taba cewa “sharrin exco ya fi na Dan Boko haram.”

Kuma ma in banda shafewar basira, yaya mutun zai sanya ran cewa zai iya kulla amana ko samun adalci daga mutumin da ka zauna ka kulla ha’inci da rashin amana da shi? Wannan tunanin na daya daga cikin abinda ke ba ni mamaki daga ‘yan siyasar mu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

NAF begins inquiry into alleged killings of civilians by Airforce pilot

The Nigerian Airforce has begun investigations into the alleged killing of civilians in Kamadougou Yobe State by an Airforce pilot. In a statement on Friday...

Yanzu haka cikin daren nan ‘yan bindiga sun afkawa garin Tangaza

LABARAI DA DUMI-DUMIN SU! Yanzu haka cikin daren nan 'yan bindiga sun afkawa garin Tangaza Labarai da muke samu sun tabbatar da cewa yanzu haka cikin...

Siyasa: PDP tayi watsi da tsagin Aminu Wali ta rungumi Kwankwaso

Siyasa: PDP tayi watsi da tsagin Aminu Wali ta rungumi Kwankwaso Babbar jam'iyyar adawa ta PDP ta sanya ranar gudanar da zaben sabbin shugabanninta na...

Abdulaziz Ganduje ya kai karar mahaifiyarsa Gwaggo EFCC kan batun almundahana

Babban dan Gwamnan Kano, Abdulaziz Ganduje ya maka mahaifiyarsa Hafsat Ganduje gaban hukumar yakibda yiwa tattalin arziki zagon kasa ta EFCC akan zargin da...

Barawon Motar Gwamnati Ya Shiga Hannu A Katsina

Barawon Motar Gwamnati Ya Shiga Hannu A Katsina. Rundunar Yan Sanda ta Jihar Katsina ta samu nasarar chafke wani mai suna Hayatu Bishir da ake...
%d bloggers like this: